Kamfanin takin Dangote zai bunƙasa noma a Nijeriya – NACCIMA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da aikin gona ta Nijeriya (NACCIMA) Olusola Obadimu, ya ce, kamfanin takin urea na Dangote zai bunƙasa cigaban noma a ƙasar.

Obadimu ya bayyana haka ne ranar Asabar a Legas ta hanyar wani rahoto daga ziyarar ban girma da ya kai kamfanin takin Dangote da ke unguwar Ibeju Lekki.

Ya bayyana cewa, aikin zai kuma tabbatar da samar da abinci da kuma samar da guraben ayyukan yi ga ’yan Nijeriya da sauran ’yan Afirka kai tsaye da kuma a fakaice.

“Babban maqasudin ziyarar shi ne don jin daɗin tasirin aikin da kuma rukunin Dangote ke yi, da kuma ta yadda za a yi a kan tattalin arzikin Nijeriya da kuma tabbatar musu da goyon bayan NACCIMA a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

“Ƙaddamar da wannan babban aikin takin zamani na urea a Afirka zai taimaka sosai wajen bunƙasa ayyukan noma ko shakka babu.

“Hakan zai yi tasiri a harkar kasuwanci a Nijeriya idan ana maganar noma da kuma bunƙasa arzikin cikin gida (GDP) daga wannan ɓangare.

“Dole ne a yaba wa kamfanin Dangote saboda gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen haɓaka tattalin arzikin Nijeriya,” inji shi.

Vishwajit Sinha, Manajan Darakta na Takin Dangote ya yaba wa tawagar NACCIMA bisa irin goyon bayan da ƙungiyar ke ba wa ajandar bunƙasa masana’antu a ƙasar.

Ya sake nanata ƙudirin kamfanin na bunƙasa ɓangaren noma ga ƙasar nan bisa tsarin Ɗorewar Muhalli (ESG).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *