Kamfanin Turkiyya zai fara noman zamani a Zamfara don bunƙasa harkar noma

Daga BELLO A. BABAJI

Sanannen kamfanin Turkiyya mai suna ‘Direkci Group’ zai fara aiki noman zamani da haɗe kai da gidajen gonaki a Jihar Zamfara don bunƙasa harkokin noma.

A ranar Asabar ne Darakta-Manaja na kamfanin, Nurullah Mehmet ya jagoranci wata tawaga zuwa ofishin Gwamna Dauda Lawal dake gidan gwamnatin jihar.

Kamfanin ya ƙudiri aniyar inganta harkar noma a jihar ta hanyar samar da auduga da rake da kuma waken suya a ma’auni mai girman gaske.

Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, kamar yadda ya fitar a wata takarda, ya ce kamfanin za ta gabatar da tsare-tsare na zamani wajen yin aikin gona da amfani da fasahar zamani a gidajen gona da kiwon kaji wanda hakan zai taimaka wajen samar da alfano mai girma ga al’ummar jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Dauda ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta tabbatar da yalwar abinci da samar da damanmakin ayyukan yi ga al’umma a jihar.

Ya ce hakan wani ɓangare ne na alƙawarin da ya ɗauka a lokacin da ya ke yaƙin neman zaɓe.

Gwamnan ya kuma ce su na da burin samar da kayayyakin aikin noma na zamani shi ya sa suka amince da karɓar masu zuba hannun-jari.