Daga AMINA YUSUF ALI
Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanonin siminti na Ɗangote da BUA suna kashe kaso 41.33 na cinikinsu wajen samar da wutar lantarki da sayen makamashi.
A yayin da shekarar nan ta 2022 ta raba, waɗannan manyan kamfanonin Sumuntin da suka fi kowanne a Nijeriya Ɗangote da BUA sun kashe kimanin Naira biliyan 173.537 a kan samar da wutar lantarki da makamashi. Wato kaso 41.33 daga cikin jimillar kuɗaɗen cinikin da suka yi tun daga farkon shekarar zuwa wannan lokaci, Naira biliyan N419.965.
Wato abinda kamfanonin biyu suka kashe ya qaru da kaso 38.34 a kan Naira biliyan 125.44 da suka kashe a iya wannan lokacin a shekarar bara ta 2021.
Rahoton alƙalumman cinikin kamfanonin na rabin shekara ya bayyana cewa, bayan an fitar da haraji, kowanne kamfani ya tashi da ribar da ta kai Naira biliyan 233.668, ashekara 2021; yanzu kuma ya zama Naira biliyan 235.026 a shekarar 2022. An samu rashin kaso 0.7%, kenan.
Wannan matsala ba ta rasa nasaba da ƙarin farashin kayan aiki wanda ya lamushe wani ɓangare na ribar.
Shi ma kuma ba ya rasa nasaba da faɗuwar tattalin arzikin ƙasa da kuma tashin farashin dala da sauran kuɗaɗen ƙasashen waje.
Wani rahoto ya bayyana cewa, kamfanin Sumuntin Ɗangoten kaɗai ya lamushe mai da wutar lantarki da ya kai darajar Naira biliyan 129 a cikin rabin shekarar 2022 kaɗai. Ba kamar Naira N98.978 ba da suka kashe a rabin shekarar 2021. Wato an samu ƙarin kashi 31.3.
Shi kuma kamfanin Sumuntin BUA ya kashe maƙudan kuɗaɗe har Naira biliyan N43.580 a kan lantarki da makamashi a cikin watanni shidda kacal na shekarar 2022. Wato an samu ƙaruwar kaso 64.66, a kan Naira biliyan 26.446 da rahoto ya bayyana an kashe a wata shidan shekarar 2021.
Kodayake, duk da wannan jewar, kamfanonin bayan sun fitar da haraji su sun samu ribar Naira biliyan 61.364 a shekarar 2022. Wato fiye da Naira biliyan 43.396 da aka samu a rabin shekarar 2021. Gwari-gwari, an samu ƙarin kaso 41.4, wanda ya nuna an samu cigaba da kaso 47.38 fiye da abinda aka samu a shekarar bara.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a kan sakamakon binciken, Manajan kamfanin Sumuntin Ɗangote, Michel Puchercos, ya bayyana cewar, duk da wannan ƙarin kuɗin, za su iya cewa cinikin shekarar 2022, sambarka!