Daga Wakilinmu
Haɗin kai shi ne wata babbar hanya mai kawo cigaba a tsakanin al’umma a cewar Malam Sani Ibrahim, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Talatar Mafara daga Jihar Zamfara, wanda a yanzu mazaunin garin Karmajiji ne a cikin ƙaramar Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ne, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Cigaban Al’ummar Hausawa mazauna birnin.
Ya bayyana dalilin da ya sa suka kafa ƙungiyar ci gaban al’ummar Hausawa mazauna Karmajiji, inda ya ce, kafin a kafa ita ƙungiyar, akan kama matasa 30 zuwa 40.
“Watarana da aka yi irin wannan kamun sai muka haɗa kanmu domin kar irin hakan ta sake faruwa.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake hira da wakilinmu bayan da ƙungiyar ta kammala taronta na mako–mako, a gidan kallon wasa da ke Karmajiji.
Dangane da abubuwan ci gaban da ƙungiyar ta kawo wa al’umma ya ƙara jaddada cewa sun katange babbar maƙabarta wadda al’ummar musulman da ke garin suke amfana da ita.
Wani abu kuma wanda ba duka ne suke yi ba domin kuwa wani ma al’amarin ya share ma gidansa abin yana matuƙar yi masa wahala. Amma su suna yin aikin gayya inda suke tsaftace muhalli da kuma gyara magudanan ruwa, saboda kaucewa yiyuwar aukuwar ambaliyar ruwa wadda ita ma wata matsala ce mai zaman kanta, ko kuma kamuwa da annobar kwalara wadda rashin tsaftace muhalli na daga cikin dalilan kamuwa da ita.
Ya ce ba kowanne Bahaushe bane ake amince ma shi da ya zama ɗan ƙungiya kai tsaye ba, sai anyi binciken yadda halin sa yake, idan an gamsu daga nan sai a amince ma shi ya zama ɗan ƙungiya.
Ƙungiyar dai kamar yadda ya ce an kafa shekaru shida da suka gabata an kuma yi mata rajista, yana kuma da wuya a iya nashi sanin a ce har Bahaushe ya kafa ƙungiya ace,ta wuce shekara biyu ko uku, amma ga shi tasu ƙungiyar tasu har ta kai shekara shida. Duk kuma wani matakin daya dace su ɗauka domin ƙungiyarsu ta cigaba da ɗorewa a matsayin tsintsiya ɗaya maɗaurinki ɗaya za su ɗauka.
Bakura ya ƙara da cewa sun shiga koyon sana’oi su kansu domin su samu hanya madaidaiciya wadda za su taimaka wa rayuwarsu.
Sarkin Husawan Karmajiji Muhammadu ɗan Ali shi ma ya furta ta bakinsa kan shi garin na Karmajiji, inda ya ce, yana mai matuƙar farin ciki dangane da kafa ita ƙungiyar, inda kuma yayi kira da mambobinta su bada haɗin kai domin a samu ci gaba ta amfanuwa hanyoyi daban-daban.