Kannywood: Babban Kwamandan Hisbah ya watsa wa Shugaban Hukumar Finafinan Kano ƙasa a ido

Daga WAKILINMU a Kano

A daidai lokacin da Shugaban Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba Afakallahu, bai halarci taron rantsarwa da liyafar cin abincin dare da Gwamnan Jihar Kano, Dr.

Abdullahi Umar Ganduje, ya shirya wa sababbin zaɓaɓɓun shugabannin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa (MOPPAN) a Gidan Gwamnatin Jihar Kano ba, shi kuwa Babban Kwamandan Hisbah na Jihar ta Kano, Sheikh Harun Muhammad Ibn Sina, ya halarci taron ne, inda har ma gabatar da addu’o’i a wajen gangamin, ya na mai sanya albarka ga masu sana’ar ta shirya finafinan Hausa a Kano da ma ƙasa bakiɗaya.

Idan dai za a iya tunawa, rahotanni sun nuna cewa, alaƙa tsakanin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood ta yi tsami tsakaninsu da Gwamnatin Gwamna Dr. Ganduje, duk da kasancewar shine gwamna mafi karrama masu sana’ar shirin fim ta hanyar ba su muƙamai daban-daban baya ga jan su a jika.

A cikin muƙaman da Ganduje ya naɗa ’yan Kannywood akwai shi kansa Afaka a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Rashida Adamu Maisa’a a matsayin Mai Taimaka Masa ta Musamman da Abdullah Alkenana a matsayin Darakta Janar na Ƙawata Birni da Kwarzanta shi da Yahanasu Sani a matsayin Mai Taimaka Wa Gwamna ita ma da Ishaq Sidi Ishaq a matsayin Babban Mai Taimaka Wa Gwamna Kan Ƙirƙirar Fasaha da sauransu.

Kazalika, gwamnan ya ɗauki nauyin bai wa ɗaruruwan ’yan masana’antar horo na musamman kan sana’ar tasu, wanda Kamfanin Moving Image ya jagoranta.

To, amma duk da irin wannan karamci da Gwamna Ganduje ya yi wa Kannywood an shiga mamakin yadda kuma mummunar adawa ta shiga tsakaninsu da gwamnatinsa, inda an shaida yadda a lokacin Babban Zaɓen 2019 suka juya wa takararsa baya har ma suka fitar da wata waƙa mai taken ‘Na Gwaggo’, wacce masu lura da al’amuran yau da kullum su na cewa, ta yi matuqar tasiri kan yadda gwamnan ya sha da ƙyar a lokacin zaven, inda ake kallon cewa, da ƙyar ya samu ya yi tazarce.

Sai dai kuma bincike ya ƙara nuna cewa, ba za a iya rasa danganta wannan gaba tsakanin Gwamnatin Ganduje da ’yan Kannywood ba kan yadda Afaka ya riƙa kama su, ya na jefa su kurkuku kan laifukan da su ke iƙirarin cewa, ba su aikata ba, musamman idan aka yi la’akari da ’yan fim ɗin da ya sa aka ɗaure, waɗanda ake zargin cewa, saɓani ne na ƙashin kansa kawai a tsakaninsa da su, amma ba wai don sun aikata laifukan a zahirance ba.

Yayin liyafar da Gwamna Ganduje ya shirya wa ‘yan Kannywood a Gidan Gwamnatin Kano

Misali a nan shine, Afaka ya sa an kama Darakta Sunusi Oscar a kan zargin sakin waƙar da ba a tace ba, duk cewa ba shi ne furodusan waƙar ba, ba shine ya yi dillancin waƙar ba kuma ba kamfaninsa ne ya ɗauki nauyinta ba.

Haka nan an kama Darakta Mu’azzamu Idi Yari akan zargin ya fita aiki ba tare da izinin hukumar ba, duk da cewa, shi ma ba shine furodusan fim ɗin, illa dai kawai a na zargin don ya samu saɓani da wata mutuniyar Afakan ce a lokacin ɗaukar fim ɗin.

A ƙa’ida ta shirya finafinai, furodusa ne ke da haƙƙin mallakar kowane izini kan fim ko waƙa, ba darakta ba. Haka nan kamfani ko ɗan kasuwa ke da izinin sakin fim ko waƙa, amma ba darakta ba.

Bugu da ƙari, an ga yadda ta raincaɓe tsakanin mawaƙi Naziri Sarkin Waƙa da Hukumar Tace Finafinan, inda har aka kama shi a ka kai shi kurkuku. Da yawa su na mamakin cewa, an yi matuƙar sakaci da aka bari alaƙar ta yi lalacewar hakan, saboda irin kyakkyawar alaƙar da ta ke akwai tsakanin mawaƙin da gwamnatin, inda a ƙarshe aka zargi hukumar da bari dangantaka ta yi mummunan tsami haka, saboda wata buƙata ta son rai.

Binciken Blueprint Manhaja ya nuna cewa, hatta Fadar Shugaban Ƙasaasa ta damu da yadda alaƙar Gwamnatin Kano ya ke neman lalata dangantakar jam’iyyar mai mulki, APC, da ’yan Kannywood, waɗanda suka fara janye jikinsu daga gare ta su na yin tururuwa zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Wannan ya kai ga gudanar da bincike ta bayan gida kan lamarin, inda a ƙarshe aka yi ittifaƙin cewa, Hukumar Tace Finafinai ta Kano ce ta haifar da wannan matsalar, domin su kansu waɗanda aka riƙa kamawa ɗin ba su daha cikin ’yan fim ɗin da ake kallo a matsayin marasa tarbiyya. “To, idan haka kuwa, me ya janyo sai waɗannan za a riƙa kamawa,” inji wata majiyar Gidan Gwamnati ga Blueprint Manhaja, wacce ta nemi a sakaya sunanta.

An ce, shi kansa Gwamna Ganduje ya fusata kan yadda ya kyautata wa ’yan Kannywood, don a tsaftace masana’antar, amma a ƙarshe ya dawo ya zama abin zunɗe a wajensu. Wannan ya sanya shi fara tunanin daga dukkan alamu ya ɗauko mugun hannu ne a cikinsu, domin maimakon ya samu yabo a wajensu, sai ya koma ya na shan bugu.

Rahotanni sun tabbatar wa Blueprint Manhaja cewa, hakan ne ya sanya aka koma teburin sasanci tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Ganduje da kuma ’yan Kannywood, inda a ƙarshe a ka yanke shawarar kakkaɓe ikon Afaka ta hanyar naɗa ɗaya daga cikin dattawan masana’antar fim, wato Malam Khalid Musa, a matsayin Babban Mai Taimaka Wa Gwamna Kan Harkokin Kannywood, wanda a ka ɗora wa alhakin sa idanu kan dangantakar masana’antar da gwamnati ta yadda za a cire son zuciya da kuma mugun nufi a tsakani ba tare da kuma an bar rashin tarbiyya a cikin sana’ar ba.

Bugu da ƙari, gwamnatin ta mayar da Hukumar Tace Finafinai ƙarƙashin umarnin ofisoshin Malam Khalid da kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai, waɗanda za su riƙa yin aiki tare, don tabbatar da an aikata abin da ya dace ba tare da an kauce wa doka ba, sannan kuma a kare buƙatun al’ummar Jihar Kano na gaskiya ba tare saka son zuciya ba ko nuna ƙiyayya ba.

A na ganin cewa, wannan kyautatuwar alaƙar ne ya sanya Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Ibn Sina, wanda alhakin hukumarsa ne sanya idanu kan rashin tarbiyya da rashin ɗa’a a jihar, ya rungumi wannan sulhu, duk da cewa, a na kyautata zaton Afaka bai so hakan ba, idan aka yi la’akari da yadda ba a ga ƙuyarsa ba a dukkan tarukan da aka gudanar.

Wani sashe yayin liyafar

Sheikh Ibn Sina ya gabatar da doguwar addu’a a wajen taron yana mai roƙon Allah da ya inganta dangantakar masu shirya fim da Gwamnatin Kano, domin amfanin Musulunci da Musulmi, kuma ya roƙi Allah ya sanya albarka a cikin sana’ar shirin finafinan Hausa a jihar da ma ƙasa bakiɗaya. A ƙarshe ya sanya albarka ga waɗanda Gwamna Ganduje ya sake bai wa muqamai a wajen taron daga cikin ’yan Kannywood, waɗanda suka haɗa da Jarumi Mustapha Naburaska a matsayin Mai Taimaka Wa Gwamna Kan Yaƙi da Farfaganda da kuma shi Malam Khalid, wanda a yanzu shi ke da alhakin kula da harkokin masana’antar bakiɗaya daga ɓangaren gwamnati.

Masu lura da al’amuran yau da kullum na kalllon wannan mataki na shehin malamin a matsayin watsa ƙasa a idanun Babban Sakatare Afaka, domin idan gyaran tarbiyya ake magana, Hukumar Hisbah ta na gaba da Hukumar Tace Finafinan Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *