Kannywood ce ta biyu wajen samar da aikin yi a Nijeriya – MOPPAN

Daga AISHA ASAS a Abuja

Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Ƙasa (wato MOPPAN), Dr. Ahmad M. Sarari, ya bayyana cewa masana’antar Kannywood masana’anta ce da ta ke da yawan guraben aiki kuma ita ce ta biyu wajen samar wa matasa aikin yi a Nijeriya.

Sarari ya faɗi hakan ne a cikin jawabinsa yayin da tawagar ƙungiyar ta kai wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ziyara a gidan gwamnatin jihar da ke Lafiya a ranar Talata 21 ga Satumba, 2021.

Dr Ahmad Sarari ya bayyanawa gwamnan yadda aka ƙyanƙyashe masana’antar ta Kannywood da kuma yadda masana’antar take bada gagarumar gudummuwa wajen wayar da kan al’umma da kuma taimakawa gwamnati ta fuskar siyasa da bayyana manufofin gwamnati.

“Masana’antar shirya fina-finai ta Arewa wadda aka fi sani da Kannywood, ta samo sunan ta ne a shekara ta 1999, shekaru biyu kafin samar da sunan masana’antar shirya fina-finai ta kudu, wato Nollywood.

“An samo kalmar Kannywood daga Ƙamus ɗin ‘Oxford’ a shekarar 2019, kuma ita ce masana’anta ta biyu a jerin masana’antun da su ka fi ɗaukar ma’aikata, wadda ta samar da ayyukan yi ga mutane sama da 700,000 waɗanda suke ci, suke sha a ƙarƙashin masana’antar. Saboda haka Kannywood za ta iya zama ta biyu a jerin masana’antun da ke samar da aikin yi bayan aikin noma.”

Shugaban ya kuma bayyana masana’antar a matsayin wata hanya ta bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya, inda ya bayyana masana’antar a matsayin ta biyu wajen samar da kuɗin shiga bayan ta masu shirya fina-finai cikin harshen Yarabanci. Ya ce masana’antar ta na samar da harajin da ya kai aƙalla Dala miliyan 180 duk shekara.

Duk a cikin jawabin nasa, ya bayyana cewa ƙungiyar ta MOPPAN ta samu rajista da CAC a shekara 2004, inda ta kasance wata rumfa ga duk wanda ke harkar fina-finai a kowane ɓangare a arewacin Nijeriya. Kuma ita ce ƙungiya ɗaya tilo a Arewa da Gwamnatin Tarayya ta san da zamanta.

Dr Sarari ya ce manufar ƙungiyar dai ita ce; inganta harkar fina-finai ta hanyar samar da ilimi da kuma ƙwarewa ga ‘ya’yanta, da ma wasu daban.

“Masana’antar shirya fina-finai masana’anta ce da ke taimakawa wajen samun kuɗin shiga ga Nijeriya, hanya mai ƙarfi wajen tallata manufofi a siyasance, hanyoyin samun kuɗaɗe, kuma hanyar haɗa kan al’umma, domin MOPPAN na da rassa a dukkan jihohin arewacin Nijeriya 19 har da Birnin Tarayya Abuja”.

A jawabin nasa, Dakta Ahmad ya bayyana goyon bayan su akan ƙudurin gwamnan na samar da kafar nishaɗanwa da ya qudiri aniyar samarwa a Jihar Nasarawa, kamar wurin shirya fina-finai da aka yi wa laƙabi da ‘Farin Ruwa Film Village’ da kuma katafaren wurin shaƙatawa na ‘Keana Salt Lakes’ da kuma babbar sinima ta ‘Canal Olympia’ da zai gina a Karu.

Dr Sarari ya bayyana gwamnan a matsayin mutum mai son ci gaban matasa da ƙarfafa musu gwiwa wajen samar musu da ayyukan yi, sannan wanda ke son ci gaban harkar masana’antar shirya fina-finai.

Sarari ya kuma tabbatar wa gwamnan da cewa masana’antar su ta masu shirya fim da mawaƙa za su ba shi cikakken goyon baya da haɗin kai son ganin ya kai ga nasara wajen aiwatar da ƙudirorinsa.

Shi kuwa a cikin jawabin sa, Gwamna Abdullahi A. Sule na Jihar Nasarawa, ya bayyana wa tawagar tasu cewa a shirye yake ya mayar da jiharsa cibiyar gudanar da harkokin fina-finai, musamman ma ta Hausa.

Gwamnan ya ce ko shakka babu ya na alfahari da matasa masu shirya fina-finai, musamman ma da ya kasance suna amfani da wannan damar da Allah Ya ba su, har su zama wasu fitattun mutane a cikin al’umma.

Ya ce, “Ina matuqar alfahari da yadda nake ganin masu shirin fim, ko kuma ko wace sana’a, musamman ma da suke amfani da damarsu, har su zama wasu mutane da ake alfahari da su.

“Amma don na ga ɗan mai kuɗi ya zama wani a rayuwarsa, hakan bai cika burge ni ba, domin matashin da ke da ƙaramin ƙarfi, sai ya ci kwakwa sannan ya zama fitacce. To, shi ya sa nake son tallafa mu su, saboda duk matsayin da su ka taka a rayuwa, ba za su taɓa mantawa da kai ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, ƙofarsa a buɗe take ga dukkanin masu shirin fim na Kannywood. Ya kuma yaba da tsare-tsaren ƙungiyar MOPPAN, inda ya amince cewar zai ɗauki nauyin babban taron ƙungiyar MOPPAN da za a yi nan da makwanni kaɗan.

“Na ji daɗi matuqa da ganin fuskokin da nake jin daɗin ganinsu a cikin fina-finai, hakan ta sa nake tabbatar muku da cewa zan yi iya ƙoƙarina wajen samar da ci gaban da duk ake buƙata, matuƙar ku ma za ku jajirce. Saboda haka, za mu ɗauki nauyin taronku da ku ke shirin yi da yardar Allah,” cewar Gwamnan na Jihar Nasarawa.

Kan batun bayar da horo ga ‘ya’yan masana’antar kuwa, gwamnan ya ƙara tabbatar da cewar za a ba wa MOPPAN damar haɗin guiwa da makarantar koya fim ta tarayya (NFI) dake Jos, domin horas da masu shirin fina-finai na Jihar Nasarawa.

Game da samar wa Ƙungiyar MOPPAN katafaren ofishi kuwa, gwamnan ya amince da buƙatar a take. Gwamnan ya ƙara da cewar ya na neman haɗin guiwar MOPPAN da ƙwarewarta wajen ƙarasa da bunƙasa cibiyar shirin fina-finai ta zamani a Farin Ruwa, wato ‘Farin Ruwa Film Village’ da gwamnatinsa ta fara.

Tun da fari dai Shugaban na MOPPAN ya ce, ko shakka babu Kannywood ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, za ta yi kyakkyawar haɗin gwiwa da Gwamnatin Jihar Nasarawa, domin haɓaka harkokin fina-finan Hausa, tare da wayar da kan mutane akan alfanun haɗin kai da kyakkyawar zamantakewa.

Domin samar da kyakkyawan yanayin haɗin gwiwar, Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Sule, ya karrama ƙungiyar ta MOPPAN da lambar yabo, a yayin da ita ma MOPPAN ta rama biki, tare da karrama gwamnan, a matsayin ‘Jagoran harkar fina-finai na Nijeriya.’

Taron dai ya samu halartar wasu daga cikin shugabannin na MOPPAN na ƙasa, waɗanda su ka haɗa da Alhaji Bala Kufaina, Ma’aji na Ƙasa, da Al-Amin Ciroma, Kakakin ƙungiyar.

Sauran sun haɗa da Darakta Ishaq Sidi Ishaq, memba a Kwamitin gudnarwa na MOPPAN, Dr. Ahmed S. Bello, Sakataren Kwamitin Zaɓen MOPPAN, da kuma Darakta Kamal S. Alkali. 

Har ila yau, akwai jarumai kamar Abdullahi Karkuzu Jos, Malam Magaji Mijinyawa, Hajiya Hadiza Muhammad, Amina Amal, Bilkisu Abdullahi da kuma tawagar ‘yan wasan Jihar ta Nasarawa.