Kano 2023: Za mu inganta ilimi da yashe dam-dam a Jihar Kano – Balarabe Rufa’i

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

A cigaba da zagayawa, don ƙara neman goyon bayansa ga al’ummar ƙananan hukumomi 44 da suke Jihar Kano, ɗan takarar kujerar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Hon. Balarabe Rufa’i, ya alƙawaranta cewa, idan ya samu nasara zai inganta harkar ilimi da yashe dam-dam da ke akwai a jihar don inganta harkar noma da sauransu.

Ya ce babu abinda ya fi a yanzu face matasa da sauran al”umma su tashi tsaye don zaɓar wanda zai kawo masu cigaba da canje-canje don cigaban yankinsu da rayuwarsu.

Ɗan takarar gwamnan ya kuma ƙudurci kawo sauyi a vangaren ilimi da ya ce jihar ta zama koma baya a ɓangaren, duk da gwamnati tana ikirarin cewa tana bada ilimi kyauta, a cewarsa.

Rufa’i bai gushe ba sai da ya roƙi jama’ar Ƙunci da Tsanyawa da su saka shi cikin addu’a don samun nasara musamman a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan.

Haka kuma tawagar ɗan takarar gwamnan sun shaida wa mutanen Ƙunchi da Tsanyawa cewa lallai ba za su ba su kunya ba idan Allah ya ɗan talarar nasara.

Kazalika tawagar ta roƙi jama’ar ƙananan hukumomin biyu da su yi duk wanda suke da ra’ayi amma su kasance masu riƙe amanar zaɓar Hon. Balarabe Rufa’i a matsayin gwamnan jihar Kano a zaɓe mai zuwa in Allah ya kaimu lafiya.

Kuma tawagar da darakta kamfe na Hon. Balarabe Rufa’i sun ƙara tabbatar wa mutanen Ƙunchi da Tsanyawa cewa su je su duba zaƙaƙuran matasan da suke da sha’awar tsayawa takarar majalisar jiha da tarayya don a ba su fom kyauta saɓanin yadda ake saida shi da tarin kuɗi har Naira miliyan biyar, amma Hon. Balarabe Rufa’i ya shiga ya fita don ɗaukar nauyin duk saya wa duk wanda zai tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC kyauta a kaf ƙananan hukumomin 44 da huɗu da ke Kano.

Su ma da suke nasu jawabin yayin ganawa da tawagar ɗan takarar gwamnan, shugabannin matasan na Ƙunchi da Tsanyawar Hon. Isah Ayuba Ƙunchi da ake wa laƙabi da (Rochas), ya ce  yanzu haka su a shirye suke da su mar wa wannan tafiya baya amma da sharaɗin riƙe amanar da aka ɗaukar masu na inganta rayuwar al’ummarsu ta Ƙunchi kamar yadda aka alƙawaranta tun farko.

Rochas ƙunchi ya kuma ce maganar yashe dam na Ƙunchi idan har wannan gwamnati ta kafu aka yi masu wannan aiki kaɗai ya wadatar da su, saboda tunda aka kafa  wannan dam ba a taɓa yashe shi ba, don haka za su yi bakin ƙoƙarin su don mara wa tafiyar baya ta kai gaci.

Shi ma Alhaji Kabir ‘Yargwanda ya yi matuƙar nuna farin cikinsa bisa ganin dukkan Waɗanda suka zo don neman goyon bayan jama’ar ƙaramar hukumar Tsanyawa ‘yan gwagwarmaya ne da aka saba yi wa al’umma hidima.

Saboda haka ne ma ya ce lallai za su ƙoƙarta wajen ganin an samu tafiya mai inganci a Ƙaramar Hukumar Tsanyawa musamman da ƙudurin mara wa Maigirma Kwankwaso baya a matakin takarar sa ta shugaban ƙasa. Don haka sun ji sun kuma gani za su yi wannan tafiya ɗari bisa ɗari.