Kano ta Tsakiya: Ni na sa kaina sayen fom, ba Ganduje ba – Sanata Lado

“Na shiga halin dimuwa a lokacin da na karanta wani labari a jaridun politicsdigest.ng da alfijir.com.ng da wasu kafafen yaɗa labarai. Wanda aka wallafa a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2022. A cikin labaran an rawaito Malam Ibrahim Shekarau ya ce: Mai girma Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ba ni umarnin tsayawa takarar Sanata na yankin Kano ta tsakiya. Duk da dai ban fiye fitowa fili na yi ce-ce-ku-ce a harkar siyasa ba, kuma na so na kama bakina na yi shiru don kare mutuncina, amma gudun kada shirun nawa ya sa wasu su zaci labarin gaskiya ne, shi ya sa ya zama dole na tanka”

A kan wancan maudu’i nake so na mayar da martani kamar haka:

  1. A matsayina na Musulmi, ina rantsuwa da Al-Ƙur’ani mai girma cewa, Mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba shi ya ba ni umarnin tsayawa takarar Sanata Kano ta tsakiya ba. Sannan ikirarin cewa, Gwamna Ganduje ya umarce Ni da na sayi fom ɗin takara, ba gaskiya ba ne ba. Wannan batu ƙarya ce tsagwaronta, kuma ƙirƙirarren zance ne da aka ƙirƙiro don a ɓata mana suna daga ni har Mai girma Gwamna a idon duniya.
  2. Na yi nufin tsayawa takara ne don ƙashin kaina sakamakon muradin dubban magoya bayana da kuma jan ra’ayi daga mutanen kirki na jihar Kano da mutanen Kano ta tsakiya. Amma abinda ya faru, na sanar da Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje muradinna na tsayawa takarar bayan na yanke shawarar yin takarar, kuma bayan mana sayi fom ɗin takarar, ba kafin na saya ba.
  3. Yana nan a tarihi cewa, a cikin lokacin da nake riƙe da muƙamin Sanata a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015 na yi ayyuka guda 113. Daya daga cikin manyan ayyukana ita ce gadar Kundila wacce ta ci Naira biliyan 2. 5 wacce ake kira da sunana, Gadar Lado. Duba da irin ayyukan da kuma burin al’ummar Kano na son cigaba ya sa suka dinga kirana na fito takara. Domin sun san na yi kuma sun gani har sun yaba da ayyukana da na yi. Misali, titin Kano zuwa Katsina wanda ya ɗan yi tafiyar hawainiya wajen shekaru bakwai kenan, sannan akwai ginin gidaje 600 a ƙaramar hukumar Dawaki Tofa banda harkar lafiya, da ilimi, da sauransu.
  4. “Na yi imani mulki na Allah ne. Kuma zai iya ba wa duk wanda Ya ga dama. Don haka, zancen wai an yi wa wani jagora ko an ba shi umarni duk bai taso ba.
  5. Na cika da mamaki da ba a gode min a kan yadda na amince da tilasta min da aka yi na haƙura da takarata a shekarar 2019 na bar wa Malam Shekarau wanda ya shigo jam’iyyar APC kwana bakwai kacal, gabanin zaɓen fidda gwani na cikin jam’iyyar. A haka na bar masa duk da na riga na sayi fom ɗin takara kuma an yi min alƙawarin ba hamayya. Haka muka haƙura da ni da dubban magoya bayana saboda ganin girman Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma jam’iyyarmu.

Kuma sakamakon haka, daga ni har magoya bayana ba wanda ya yi barazanar barin jam’iyyar ko ƙoƙarin ta da fitina, ko tarzoma ko zagin Maigirma Gwamna, ko iyalansa ko gwamnatinsa. Don haka, ba adalci a cikin umarnin cewa, na sake haƙura da takarata na sake bar wa Malam Ibrahim Shekarau ya tsaya takara? Kuma shi kaɗai ba hamayya . Shin wannan adalci ne ko demokraɗiyya? Wallahi ba ko ɗaya daga ciki.

  1. Yankin sanatoriya na Kano ta tsakiya ita ce yanki ma fi girma daga cikin yankunan. Yana dauke da fiye da mutane miliyan 10. Don haka tana buƙatar wakilci sosai ba wai a hana kowa takara a ce an ba wa mutum guda kuma ba hamayya.

7 – A kan haka, nake kira ga mambobin jam’iyyarmu masu adalci da su tsaya su ajiye duk wani son rai su rungumi wannan katafariyar jam’iyya tamu da gwamnatin Maigirma Abdullahi Umar Ganduje. Duk da na san yanzu Gwamna yana da abubuwa da dama da suka ɗauke masa hankali, don haka ‘yan jam’iyyarmu kowa ya manta duk wani savani. Mu zo mu tallafa wa jam’iyyarmu da Gwamna Ganduje domin ya cigaba da tabbatar mana da dimokuradiyya.

A saƙona na ƙarshe nake cewa, ina roƙon Allah SWT da ya sa a yi zaɓe na adalci kuma a yi lafiya qalau. Kuma ina yi wa APC addu’ar samun nasara a zaɓe mai zuwa.

Na gode
Allah ya albarkace ku.
Sanata Basheer Garba Mohammed (Lado)