Kansilan Guringawa, Muslihu Yusuf Ali ya ƙaddamar da shirin bada ilimi kyauta ga marayu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ƙarshen makon jiya ne kansilan Kano, Honorabul Muslihu Yusuf Ali ya ƙaddamar da raba tallafi ga marayu 10 da aka samar wa gurbin karatu da ɗaukar nauyin su a ‘Ihya’us Sunna Science and Commercial College’ tare da bada tallafin N20,000 don ɗinka masu kayan makaranta.

Shirin wanda ke ƙarkashin kwamitin Hajiya Bilkisu Yusuf Ali da ake wa laƙabi da ‘Guringawa Education Promotion Committee’ a turance zai duba makarantun kuɗi da ke cikin mazaɓar don samun gurbi na malamai da ɗalibai, sai kuma gidauniyar kansila ta bayar da tallafi.

Haka kuma Muslihu Yusuf Ali, a ƙarƙashin gidauniyar sa ‘Charity and Development Foundation’ zai ɗauki nauyin kayan karatu da bada rigunan makaranta kyauta.

Kana zai tabbatar an cike guraben makaratun firamare da sakandare da ke faɗin mazaɓar da kuma yara da ba sa zuwa makaranta, su ma an ba su tallafin kayan karatu da kayan sawa na makaranta.

Bugu da ƙari, Homorabul Muslihu Yusuf ya jagoranci wata tawagar manyan baƙi da ‘yan kwamiti zuwa cibiyar rajistar JAMB ta ‘Prestigious CBT Centre’ inda ya ɗauki nauyin yara 50 da don a yi masu horo na musamman kan yadda ake rubuta jarabawar JAMB da na’urar kwamfuta. Inda tallafin ya laqume kuɗi aƙalla naira 150,000.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Sakatariyar Ilimi ta ƙaramar hukumar Kumbotso, Hajiya Ramlat Muhammad da Babban mai ba da shawara akan harkokin tsaro na Kumbotso, Honorabul Muhammad Auwal da Hajiya Bilkisu Yusuf Ali, wanda ita ce Shugabar kwamitin haɓaka harkar ilimi a gundumar Guringawa, da Kodinetar da ke kula da harkokin ilimin ƙananan yara, da Barista Nura wanda ya wakilci ƙungiyoyi a wajen taron.

Sauran waɗanda suka halarci ƙaddamar da tallafin sun haɗa da ɗaukacin masu taimaka wa kansilan kan sha’anin gudanar da ayyukan sa, da kuma dukkan ‘yan kwamitin haɓaka harkar ilimi na gundumar Guringawa, da jam’an tsaro da kuma ‘yan jaridu.