Kansilan Kano, Hon. Muslihu Ali, ya zama shugaban ƙungiyar kansilolin APC na farko

Daga WAKILINMU

An rantsar da Hon Muslihu Ali ne tare da wasu takwarorinsa a muƙamai daban-daban na ƙungiyar, wanda ya gudana a ranar 5 ga Fabrairun 2022 a PAMEEC LUXURY APARTMENTS da ke Abuja.

Idan da dai za a iya tunawa, Hon. Muslihu Ali, shi kansilan da ya naɗa mataimaka har su 18 don taimaka masa wajen gudanar da harkokinsa.

Ƙungiyar ta ƙunshi kansilolin APC ne masu ci daga sassan ƙasar nan, waɗanda suka aminice su haɗu su dunƙule wuri guda don taimaka wa jam’iyyarsu ta APC wajen bunƙasa da karɓuwa a yankunansu.

Bayanan bayan taro sun nuna cewa, yana daga cikin dalilan Kansilolin na kafa wannan ƙungiya kasancewar su ne suka fi kusa da al’umma, wasu lokutan kuma su ne mahaɗar jama’a da jagorancinsu.

Don haka suka ce, sun zamo tamkar wakilan kawo cigaban al’umma daidai da muradun jam’iyyarsu.

Manyan baƙi da suka halarci taron rantsarwar sun haɗa da wakilin shugaban riƙo na ƙasa na APC, Alhaji Alpha Yahaya (Danmasani of Panda), wakilin gwamnan Kogi, Hon Muktar Baje, da wakilin gwamnan Kano, Hon Abdulmajid Isa (umar mai rigar Fata), da ɗan Majalisar Wakilai daga Maiduguri, Hon Babagana Ajari da sauransu.

Barr Abubakar Muhammad Shehu shi ne wanda ya rantsar da shugabannin ƙungiyar na ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *