Kansiloli sun dakatar da shugaban ƙaramar hukuma a Neja

Bayanan da MANHAJA ta kalato daga jihar Neja na nuni da cewa, kansilolin ƙaramar Hukumar Mariga a jihar sun dakatar da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Idris Ibrahim T.O na tsawon watanni uku.

Bayanin dakatarwar na ƙunshe ne cikin wata takarda da kansilolin ƙaramar hukumar suka sanya wa hannu.

Shugaban majalisar kansilolin, Hon. Aliyu Bagga Mohammed ya bayyana wa gidan rediyon Landmark da ke Kontagora cewa, suna zargin shugaban ƙaramar hukumar da aikata wasu laifuka shi ya sa suka ɗauki matakin dakatar da shi domin bada zarafin gudanar da bincike a kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *