Kanu da Igboho: Ba cinya ba ƙafar baya

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Nijeriya na da kurarin ƙasa da ke rayuwa da bambance-bambance cikin haɗin kai. Bisa ma’anar ƙasa mai addinai, ƙabilu da muradu daban-daban amma ta ke zaune a dunƙule a matsayin ƙasar baƙar fata mafi yawa a duniya.

Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka haɗe arewaci da kudanci a 1914 a matsayin ƙasa ɗaya al’umma ɗaya!. Zuwa yanzu shekaru 107 yankin arewacin Nijeriya kaɗai bai taɓa barazanar ɓallewa daga ƙasar ba ko da kuwa saboda son cimma burin siyasa ne.

Ko lokacin da Gideon Orkar daga Binuwai ya yi juyin mulkin da ya watse, shi ya ayyana yanke wasu jihohin Arewa da nuna ya fitar da su daga Nijeriya ko inda zai iya mulka. Wannan ya nuna ba a ba shi shawarar da ta dace ba ko abun da ya kurɓa ya gaya ma sa ƙarya, domin Nijeriya ba za ta yiwu a mulke ta ba tare da yankin Arewa ba, bisa yadda hatta turawa suka mulki yankin ta hanyar sarakuna don samun yankin da tsarin shugabancinsa daga tarayyarsa har kan masu unguwanni.

Abun da ya zama mai ɗaukar hankali shi ne duk wani da ya tashi neman raba Nijeriya ya na ɗora manufar tasa ko ƙiyayyar tasa ga yankin Arewa ne. Tambaya a nan shin yankin Arewa ne ya matsa lamba a kafa dunƙulalliyar Nijeriya? A wajen neman amsar wannan tambaya za a gano abubuwa da yawa da suka haɗa da tasirin bambanci addini, ƙabilanci da vangaranci wajen wargaza dauloli da haddasa yaƙi a duniya.

Kazalika akwai wani muradin da ya sha bamban da waɗannan shi ne na tattalin arziki ko jari hujja da ke son duniya ta zama ƙarƙashin jagorancin wasu ƙasashe ko mutane ƙalilan masu yawan kuɗi da makamai. Wannan tsari ya yi kama da kashin dankali manya su danne ƙanana.

Wannan shimfiɗa ce ga gano cewa muradun ɗan rajin kafa Biyafara Nnamdi Kanu da ɗan rajin kafa Oduduwa Sunday Igboho iri ɗaya ne. Muradun a siyasance ma iri ɗaya na neman amshe ragamar madafun ikon fadar Aso Rock.

A kan lulluɓe wannan manufa da neman ɓallewa ta hanyar batun kafa ƙasar ‘yan ƙabila Ibo da ƙasar ‘yan ƙabilar Yarbawa. Wannan ya fito fili ne bayan da wasu ‘yan Arewa suka buƙaci Ibo masu son ƙasa su fice daga Nijeriya su koma ƙasar su. Nan take wasu daga cikin su suka ce ai su “INYAMURAN AREWA NE” don haka ko an kafa Biyafara ba inda za su je.

Kazalika, sai a ka ji gwamnonin Ibo na cewa su ma ba za a raba Nijeriya ba. Amsar su ta sake fitowa inda suka haɗu da gwamnonin Yarbawa da na Kudu-maso-kudu suka ce lalle mulkin 2023 ya koma yankin su. Ba mamaki in ya koma yankin su sai su tsara yadda za su kafa ƙasar tasu ta hanyar ƙuri’a bayan wargaza darajar dunƙulalliyar ƙasar a idon duniya.

Kuma masana sun ba da tabbacin hasashen gagarumar fitina ce za ta biyo bayan raba Nijeriya ko da kuwa ba a gwabza yaƙi ba. Wato ƙarshe sai duk ‘yan ƙasa na asali da ma ‘yan aware sun gwammace a sake dawowa gidan jiya. Na tabbatar akwai ‘yan Arewa da za su ce “Umma ta gaida A’isha” duk mai son tafiya ya tafi don Arewa dama ta tava zama ƙasa mai cin gashin kan ta da tattalin arziki mai ƙarfin gaske.

Da alamu Gwamnatin Jamhuriyar Benin za ta iza ƙeyar ɗan bangar Yarbawa Sunday Igboho zuwa Nijeriya bayan cafke shi ranar Litinin.
Igboho wanda ya sulale daga Nijeriya bayan yunƙurin zanga-zangar kafa ƙasar Yarbawa, ya shiga Benin da nufin arcewa zuwa Jamus sai ‘yan sanda suka kama shi a filin jirgin saman Kotono. Ɗan bangar na tare da ɗaya daga matan sa ‘yar Jamus da ke yi ma sa zagi wajen neman tserewa daga farautar da hukumomin Nijeriya ke yi ma sa bayan zanga-zanga a kusan dukkan jihohin Yarbawa da tuhumar mallakar miyagun makamai.

Igboho wanda ke son a kori dukkan Fulani daga jihohin Yarbawa, ya yi sanadiyyar fitinar da ta kawo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa. Akwai lokacin da ya jagoranci ‘yan bindiga suka shiga matsugunan Fulani da nufin murƙushe su gaba ɗaya ma a huta. Irin wannan aƙidar ko manufar ya haddasa fitinar da ta yi sanadiyyar zubar da jini da lalata dukiyar ‘yan Arewa a kasuwar Sasa da ke birnin Badun.

Tsarin Igboho tamkar Nnamdi Kanu ne a wajen ƙabilar Igbo, don nazari ya nuna akwai manyan yankinsa da ke mara ma sa baya ko ɗaukar nauyinsa. Hakanan akwai talakawa da ke shauƙin ganin ya cimma nasara. Zuwa yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta yi martani kan cafke Igboho ba. Tuni wasu ƙungiyoyin kare muradun Yarbawa ke adawa da neman dawo da Igboho Nijeriya da nuna ba za a yi ma sa adalci ba

Yanzu dai ya nuna muhimmancin hukunta duk masu neman wargaza Nijeriya ta hanyar dokokin Nijeriya. Kanu na cigaba da fuskantar shari’a a gaban Jostis Binta Nyako a babbar kotun tarayya a Abuja. Haka kuma ana sa ran Igboho ma zai gurfana gaban kotu don fuskantar shari’a bisa dokokin Nijeriya.

Haƙiƙa amfani da bayanan sirri wajen magance miyagun iri na da tasiri ainun in an duba yadda a ka cafko Kanu a Kenya ga shi yanzu kuma an cafke Igboho a Benin. Shawara ga masu son mulkin 2023 su dage da kamfen don gamsar da masu kɗa ƙuri’a su zaɓe domin yayin barazana ya wuce. Hakanan masu son raba ƙasa su haɗa kai da ‘yan majalisarsu a majalisar dokokin tarayya wajen kawo buƙatar don a yi ƙuri’a komai ya kammala salun-alun ba kare bin damo.