Kar a zargi Gwamna Buni wajen faɗuwar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa a Yobe – Injiniya Umar Ali

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, a Damaturu

An bayyana cewa rashin wakilci nagari, ta fuskar ‘yan majalisar dokokin Yobe, shugabanin ƙananan hukumomi, tare da wakilan al’umma a matakai daban-daban a matsayin tarnaƙin da ya dabaibaye jam’iyyar APC ta sha mummunan kaye, a zaɓen Shugaban Ƙasa haɗe da na ‘yan majalisun a makonnin da suka gabata a jihar Yobe.

Wannan furucin ya fito ne daga bakin ɗan takarar Gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin jam’iyyar APC da NNPP a zaɓukan fidda-gwani na shekarar 2019 da 2022, Engr. Malam Umar Ali, wanda halin yanzu na hannun daman Gwamnan jihar Yobe ne, Mai Mala Buni, a wani taron tuntuɓa da ya gudanar da magoya bayansa a babban ɗakin taron ƙaramar hukumar Bade da ke Gashu’a a Jihar Yobe.

Taron wanda ya tattaro mata da matasa a ƙananan hukumomi 6 dake Yobe ta Arewa (Zone C), domin jin ƙorafe-ƙorafen jama’a tare da ɗaukar matakan shawo kan su, ta hanyar bai wa gwamnatin jihar Yobe muhimman shawarwari don neman mafita.

Biyo bayan abubuwan da suka faru ne a lokacin zaɓen ne ya jawo cewa ya kamata a matsayin su na muƙarraban Gwamna Buni su zauna wajen nazarin gano mafita ga matsalolin da suka jawo faɗuwar jam’iyyar APC a zaɓen Shugaban Ƙasa. Ya ce, “Saboda a tarihin Jihar Yobe ba a taba samun lokacin da jama’a suka yi fishi, sun yi bore ba za su fito zaɓe ba ko kuma ba za su zabi APC ba, sai a wannan karo.”

Ya ce idan hakan ya faru dole akwai dalilai, saboda mutane ba su yi bore ba don ba su son gwamnati, ko saboda ba su son APC, face kawai jama’a sun ɗauki wannan matakin ne domin su nunawa gwamnati cewa akwai matsala don a gyara.

“Kuma Gwamna da kansa ya ji waɗannan ƙorafe-ƙorafen, inda hakan ya sa ya buƙaci muji koken al’umma tare da bin hanyoyin gyara su, wanda ga shi mun haɗu da mutane kuma sun yi bayanai da kansu, kuma zamu isar da sakon su tare da bayar da shawarwari masu ma’ana don a gyara.”

“Bugu da ƙari, mun gano cewa waɗanda suke wakiltar al’umma ne ba su gudanar da wakilci mai kyau; ba su isar da sakon al’umma irin yadda ya kamata. Wannan su ne ƙorafe-ƙorafen jama’a suke faɗa mana a dukan wuraren da muka ziyarta a fa dain jihar Yobe.”

Ya ce ƙorafin da yafi yawa shi ne irin yadda yan majalisun dokoki da shugabanin ƙananan hukumomi, sun sani mutanen su ba su da ruwan sha, babu wutar lantarki da hanyoyi a wasu wurare, amma ba za su kai wa gwamnatin jihar koken al’umma ba, illa iyaka idan sun yi ƙorafi sai matsalolin kansa ko na makusantan su.

Malam Umar ya ce, “Waɗannan matasa, da mata sune kan gaba wajen jefa ƙuri’a, inda mata suke shiga gida-gida lungu da sako wajen nemo mata su fito jefa ƙuri’unsu, amma da zarar an gama zabe shikenan ba za su sake ganin wakilan su ba, sai zabe ya zagayo. Su kuma matasa su ne masu ƙoƙari a lokacin zabe, su jefa ƙuri’a, su kasa su tsare kuma su raka, amma da zarar an bayyana sakamakon zaɓe, shikenan an bar su.”

Engr. Umar Ali ya bai wa daruruwan mata da matasan haƙuri tare da daukar alƙawarin share musu hawayen su, “Nayi muku alƙawarin zan gaya wa Gwamna Buni kokenku. Kuma ina mai jan hankalin matasa, mu natsu, saboda irin halin matsin tattalin arziki da ake ciki, babu yadda za a yi ace gwamnati ta ba kowanen mu aiki, kuma kar mu yarda da duk wanda zai mana dadin bakin yuwar hakan. Amma abin da za a yi shi ne duk lokacin da gwamnatin Yobe zata ɗauki ma’aikata, za mu shige muku gaba, mu tabbatar anyi adalci wajen saka sunan wasu daga cikin ku.”

Ya ƙara da cewa, idan gwamnati za ta bayar da tallafi ga jama’a, za su tsaya kan dole a raba zuwa kowa ya samu, ba tare da sun bari wasu sun handame wajen karkatar da tallafin zuwa tsiraru ba. Ya ce, “za mu buƙaci a bamu dama mu shiga kowane lungu don haɗuwa da jama’a wajen nemo wadanda suka cancanta mu mika masa. Suma wakilan jama’a a basu wanda za su kawo, amma zamu tsaya sai an tantance, wannan shi ne ƙudurinmu.”

“Muna ƙara bai wa jama’a haƙuri a fito a zabi wannan gwamnati a ƙarƙashin jam’iyyar APC; mu tabbatar mun zabi Gwamna Mai Mala Buni tare da yan majalisar dokoki masu rinjaye waɗanda zasu taimaka masa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba. Saboda idan muka yi kuskuren zaɓar wata jam’iyyar da ba APC ba, tamkar mun toshe wa kanmu ƙofar ci gaba ne a sama. Kuma muna da cikakkiyar damar da za mu ƙalubalance su.”

A ƙarshe Malam Umar Ali ya ja hankalin matasa su guji harkokin bangar siyasa kuma su guji haɗa hanya da baragurbin yan siyasa masu bai wa matasa miyagun kwayoyo don su yi amfani da su a lokutan zaɓuka.