Karatun ‘ya’ya mata ne mafita ga taɓarɓarewar tarbiyya – Hajiya Fati Jajere

iyaye ku daidaita tsakanin karatun ‘ya’ya maza da mata

Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe

Hajiya Fati Isa Jajere, ita ce shugabar gidauniyar F-Jajere Foudation, ‘yar Kasuwa ce kuma ‘yar siyasa, sannan kuma basarakiya. A tattaunawar da wakilinmu Abubakar A. Bolari, ya yi da ita, ta bayyana tarihin rayuwarta da kuma irin nasarori da ta samu. Ga yadda tataunawar ta kasance;

MANHAJA: Hajiya za mu so jin taƙaitacen tarihinki.

HAJIYA FATI: Sunana Fati Isa Jajere, ni ‘yar asalin garin Jajere ce a ƙaramar Hukumar Fune a Jihar Yobe, Arewa maso-gabas a tarayyar Nijeriya. Mahaifina Bafulatanin Jajere ne, mahaifiyata kuma Bahaushiya ce ‘yar garin Utai a ƙaramar Hukumar Wudil ta Jihar Kano. An haife ni a ranar 1 ga watan Janairu 1983 a ƙaramar Hukumar Potiskum, a nan na girma har aka sa ni a makarantar firamare ta Buraima, ina aji uku aka bai wa mahaifina sarauta a garin Gadaka ta ƙaramar hukumar Fika, sai muka koma can inda na ƙarasa firamare ɗina a can, a shekarar 1992. Da na gama sai na tafi makarantar sakandaren gwamnati ta ‘yan mata a Gadaka, na gama a shekarar 1997. Ina gamawa sai aka min aure da uban ‘ya’yana marigayi Muhammed Ibrahim Kwage, Allah ya jiƙan shi da rahama. 

Dayake ma’aikacin banki ne, aikin sa ya sa mun zauna a jihohi daban-daban, kama daga Adamawa da Gombe da Borno da Yobe da kuma Kano, har Allah ya masa rasuwa a shekarar 2011. Bayan rasuwar sa ne na yi difloma akan kimiyyar na’ura mai ƙwaƙwalwa, wato ‘Computer Science’, kuma yanzu haka ina shirin komawa na yi digiri a fannin kimiyyar siyasa in sha Allah.

Shin ko Hajiya ta taɓa samun kanta a aikin gwamnati?

Ban yi aikin gwamnati ba, ni ‘yar kasuwa ce, ina saye da sayarwa a Jihar Kano, ina da shago a Tarauni inda nake sayar da tufafi na maza, takalma, turare da dai sauransu.

A matsayinki ta wadda ta jima tana gwagwarmaya a harkokin yau da kullum, shin wane irin ƙalubale kika taɓa fuskanta?

Na fuskanci ƙalubale da yawa bayan mutuwar maigida na, ina da shekara 29 ya rasu, ya barni da ƙananan yara guda biyar, ga shi a lokacin ban ma san mene ne sana’a ba, ga shi ya bar ni da yarinya ‘yar watanni shida ina goyan ta, sannan kuma na haife ta da matsalar ciwon zuciya. A lokacin ba ni da ko dubu biyar tawa ta kaina, kuma ba wanda yake tallafa min sai Allah, sai mahaifiyata; wata rana zan tashi ba ni da ko kuɗin keke-napep ɗin da zan kai yara makaranta, wata rana ma a koro su saboda ban biya kuɗin makarantar ba. A gaskiya na shiga tashin hankali ba kaɗan ba. Wata rana mu tashi ba makamashin girki, ko babu magin sawa a abinci, ga shi nan dai abubuwa daban-daban.

Shin a yanzu kin samu ribar haƙuri da jajircewar da kika yi ne?

Gaskiya Alhamdulillah na gode wa Allah, kuma ina godewa mahaifiyata, domin da ba don jajircewar ta ba to da ina ga zan shiga tashin hankali ba kaɗan ba, saboda ita ta tallafa min har na kai na tsaya da ƙafafuna; kama daga makarantar yara, ta biya rabi na biya rabi, kuma har gobe ba ta nuna gajiyawar ta a kaina da yarana, shi ya sa nake bai wa ‘yan uwana mata shawara a daure a koyi sana’a.

To Hajiya ya maganar iyali fa yanzu?

Alhamdulillahi ina da yara biyar, maza uku, mata biyu; Muhammad Khalid da Muhammad Sani da kuma Muhammad Kabir. Sai matan akwai Hafsat da kuma ‘yar auta ta Halima.

Shin kin taɓa shiga wata ƙungiya ta siyasa ko kuma ta taimakon kai-da-kai?

Na yi aiki da ƙungiyar Atiku Care Foundation, amma na bar ta sakamakon wani dalili nawa, sai kuma ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Buhari, ta Buhari campaign Organisation a matsayin SSA ta National Women Organisation and Empowerment. sa’annan kuma na riƙe matsayin darakta ta yankina a jiha ta ta Yobe, wato 4 Plus 4. Sai kuma ƙungiyata ta Yobe Women Consensus Initiatiɓe wanda a yanzu nake haɓaka ta, sai kuma ƙungiyar Northern Nigerian Women in Politics da nake riƙe da jihohin Arewa maso-gabas.

Ko Hajiya ta taɓa fita cikin ƙasar ta Nijeriya zuwa wata ƙasar da sunan ziyarar buɗe ido ko wani na musamman? 

Na je ƙasar Saudiya, Indiya, Dubai, Kairo, Nijer; sannan kuma na je ƙasar Itofiya, wato Habasha.

Wacce ƙasa ce ta fi ba ki sha’awa a cikin ƙasashen nan da kika je?

A Gaskiya na fi son Dubai da Saudiya, saboda ina jin nishaɗi gaskiya idan na ganni a waɗannan ƙasashen.

A yanzu wane buri kike son ki cimma a rayuwarki?

Burina bai wuce na ga na inganta rayuwar matan da mazajen su suka mutu ba, musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafi rayuwarsu, da kuma yara mata marayu. Fatana in sa su farin ciki a rayuwa, sannan in ga sun amfana da ni. Abu na biyu kuma shi ne in ganni ina rayuwar aure cikin farin ciki da zaman lafiya.

Wane kalar tufafi kika fi sha’awa?

Na fi son abaya wato doguwar riga da kuma shadda mai tsada .

ɓangaren abinci fa wanne ne kika fi so?

Gaskiya na fi son abincin gargajiya fiye da kowanne abinci, musamman ma tuwon Burabisko da miyar yakuwa. 

Kina da wata alaƙa da sarauta?

ƙwarai kuwa, ni jinin sarauta ce gaba da baya. Sunan Sarauta ta Fulani, saboda bayan zamewata ‘yar sarauta, na kuma auri ɗan gidan sarauta.

Me ya birge ki har kika tsunduma harkar siyasa?

Abin da ya sa na ji ina sha’awar siyasa saboda matar tsohon gwamnan Yobe, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, irin jajircewar ta, domin mace ce mai kamar maza, ko ma in ce ta fi wasu mazan. Yadda take jan ‘yan uwa mata a jiki ba tare da ta ƙyamace su ba duk talaucin su, gaskiya hakan ba ƙaramin burge ni ya yi ba, kuma na ji ni ma zan iya koyi da ita. Mutane da dama suna ganin duk matar da ta shiga siyasa kamar ba kamila ba ce, to ba gaskiya ba ne. Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ce, hakan ne zai sa in kina da wata matsalar ‘yar uwar ki mace ita za ta fahimci mai ki ke ciki, kuma ta wacce hanya za ta taimaka da dai sauransu. 

Sannan ina kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi da a dinga damawa da mata a ɓangaren muƙaman siyasa, domin sun fi kowa jajircewa a wajen yaƙin neman zaɓe da kuma jefa ƙuri’a. A wani gefen kuma akwai ta a jinin jiki na, saboda mahaifina gogaggen ɗan siyasa ne a Jihar Yobe, domin kowa ya san shi duk inda ka kira sunan Alhaji Isa Jajere an san ɗan siyasa ne tun a lokacin NEPU yake siyasa. Bayan haka, a jiha ta ta Yobe ina ga ta hanyar siyasa ne kaɗai zan iya samun damar da zan wayar wa mata kai, kuma ta haka ne zan iya jan hankalin gwamnati ta shigo ta inganta rayuwar su. Sannan idan muka lura a wannan jiha tamu mata ba a ba su muƙamai a gwamnati ba, bayan kuma su ne suke kasawa su tsare su jira a lokacin zaɓe.

Wacce shawara za ki ba wa mata ‘yan uwanki?

Ina mai bai wa iyaye shawara, su jajirce duk runtsi duk wuya su sa ‘ya’yansu a makaranta, su samu ilimin zamani, bayan na addini da suke yi. Domin ilimin ‘ya’ya mata ba ƙaramin alheri ba ne, duk macen da ba ta da ilimi rayuwarta ba ta tafiya a saiti kamar na wacce take da ilimi. Sannan yana da kyau iyaye su gane ita ‘ya mace tana da tausayi kuma ko a gidan aure za ta amfani ahalinta da ilimin, hatta tarbiyyar ‘ya’yanta sai ya bambanta da na wacce ba ta yi karatu ba. Ina ƙara jan hankalin iyaye da su daidai ta tsakanin karatun ‘ya’ya maza da mata kar a bambanta, wani abu kuma shi ne iyaye su gane ɗorawa yara mata talla da suke yi yana jawo taɓarɓarewar tarbiyyar yaran da kuma jefa rayuwar su ga halaka, don haka mafita ɗaya ita ce bai wa ‘ya’ya mata ilimi.

Mun gode.

Ni ma na gode.