Kare kasafin 2025: Ministan Kuɗi ya nemi a yi ganawar sirri game da tallafin fetur

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Kuɗi kuma Kodineta Minista na Tattali, Wale Edun, wanda sanatoci suka dabaibaye shi da tambayoyi a lokacin kare kasafi, ya buƙaci kwamitin tantancewa da ya samar da keɓantaccen waje don bada amsoshinsu.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Ministan ya tsaya a gaban kwamitin don kare matakin aiwatar da kasafin kuɗin ma’aikatarsa na shekarar 2024.

A lokacin da Sanata Abdul Ningi daga Bauchi ta Tsakiya (PDP), ya buƙaci Ministan ya yi bayani game da yadda aka sarrafa kuɗaɗen tallafin fetur a shekarar 2024, sai Minista Edun ya ce a ba shi damar amsa tambayar ta bayan fage.

Ningi ya ce ba su samu amsar nawa ne aka samu daga tallafin man ko kuma abin da aka kashe daga bakin ministan ba, ya na mai cewa tattaunawar ba ta bayan fage ba ce.

Daga nan ne kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Sanata Olamilekan Adeola ya nemi ƴan jaridu da su ba su waje domin sauron amsoshin tambayoyinsu ga ministan a keɓance.