Wani kare a ƙasar Jamus mai suna Gunther VI ya zama babban attajiri bayan an damƙa ma sa gadonsa na biliyoyin Daloli.
An yi kiyasin cewa, karen ya zama mamallakin Dala miliyan 500, kimanin Naira biliyan 205,420,000,000 kenan, kuma yana rayuwa a wani katafaren gida, kamar yadda rahoto ya tabbatar.
Gunther VI na ɗaya daga cikin zuri’ar Gunther III wanda ya taki sa’a ya gaji ɗumbin arziki daga uban gidansa, Karlotta Liebenstein, wanda ya mutu a 1992.
Kakan kare Gunther VI ya gaji dukiyar ne shekaru 30 da suka gabata bayan ya cika burin uban gidan nasa, kamar yadda Business Journals ta rahoto.
Na tsawon wannan shekarun, tawagar masu kula da dukiyar domin tabakwaibatar da cewa, jinin kare Gunther ne kaɗai suka amfana da ita.
Ɗaya daga cikin amfanin da aka yi da dukiyar shi ne, sayen wani katafaren gida, wanda a yanzu aka saka shi a kasuwa kan kuɗi dala miliyan $31.75 (N13,044,170,000).
Wannan gida da aka ɗaga, za a sayar ba shi ne asalin gidan da karen ke rayuwa a ciki ba, domin shi wancan gidan yana Italiya ne.