Kasafin 2022: Buhari ya kasa cika alƙawarin da ya ɗauka a fannin ilimi

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Duk da alƙawarin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi a zauren taro na ƙasa da ƙasa cewar, zai ƙara kason fannin ilimi daga cikin dabtarin kasafin kuɗi na shekaru masu zuwa ya ƙaru zuwa a taƙaice kashi hamsin cikin ɗari, kuma da sannu zuwa kashi ɗari a shekara ta 2025, sai kwatsam a cikin dabtarin kasafi na shekara ta 2022 kaso da aka yi wa fannin ya faɗi warwas zuwa Naira tiriliyan ɗaya da kusan ɗigo uku ko kashi bakwai da ɗigo tara cikin ɗari, daga cikin gundarin dabtarin kasafin da ya ƙunshi zunzurutun kuɗaɗe tiriliyan goma sha shida da ɗigo talatin da tara.

Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Malama Zainab Ahmed a ranar Juma’ar makon jiya yayin da take ɓarje dabtarin kasafin a Abuja, ta ce kuɗaɗen da aka ware wa fannin ilimi sun haɗa da Naira biliyan ɗari da takwas da aka keɓe wa sashin ilimi bai ɗaya a faɗin ƙasar, tiriliyan ɗaya da ɗigo biyu na yi wa ajujuwa da makwancin ɗalibai kwaskwarima, Naira biliyan ɗari uku da cas’in da biyu somin taɓin kafa kwalejojin kimiyya da fasaha na gwamnatin tarayya, biliyan huɗu da rabi kuɗaɗen tallafi wa ɗalibai da kuma biliyan biyu na biyan alawus-alawus wa shirin malaman koyarwa na tarayya, wato Federal Teachers Scheme Allowance su guda 5,000.

Wannan shekara, an ware kuɗaɗe biliyan ɗari bakwai da arba’in da biyu, da rabi ko kashi biyar da ɗigo shida cikin ɗari wa fannin ilimi, daga cikin gundarin daftarin kasafi da ya ƙunshi zunzurutun kuɗaɗe tiriliyan goma sha uku da ɗigo shida.

Idan za a iya tunawa, a kwanakin baya ne Shugaba Buhari ya halarci wani gangami akan ilimi da shugabannin duniya suka halarta a birnin Landan  inda kowannen su ya yi alƙawarin ƙara kashi wa fannin ilimi daga cikin daftarin kuɗi na ƙasarsa.

A wajen gangamin, Shugaba Buhari ya sha alwashin ƙara kashi wa fannin ilimi daga cikin daftarin kasafin kuɗi na Nijeriya zuwa kashi hamsin cikin ɗari a cikin shekaru biyu masu gabatowa.

Shugaban na Nijeriya ya ce “Muna da yaƙinin ƙara kaso wa fannin ilimi ya zuwa kashi hamsin  cikin ɗari daga daftari, har ya zuwa kashi ɗari a shekara ta 2025, bisa kashi ashirin da shida  cikin ɗari da duniya ta ayyana”.

Gangamin na duniya akan ilimi, wanda aka gudanar da haɗin gwiwar shugabannin Biritaniya da na Kenya, Mr. Boris Johnson da Uhuru Kenyatta, ya samu tagomashin tsabar kuɗi Dalar Amurka biliyan huɗu daga cikin Dala biliyan biyar da aka yi ƙiyasi domin farfaɗo da fannin ilimi a ƙasashe marasa ƙarfin tattalin arziki, ciki har da Nijeriya.
Da yake yin tsokaci akan batun a ranar Lahadin makon jiya, shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce yana ɗaya daga cikin batutuwa da ƙungiyar za ta tattauna da gwamnatin tarayya a cikin makon idan shugabannin ƙungiyar suka hallara.

“Ina da qarfin gwiwar za mu zauna da jami’an gwamnatin tarayya a cikin satin, kuma wannan yana ɗaya daga cikin batutuwa da za mu tattauna a kai”.

“Fafutukar da muke ta yi domin bunƙasa fannin ilimi ya haɗa da ƙarin kuɗaɗe wa fannin. Idan babu wadatar kuɗaɗe a fannin, ba za a cimma wata fitacciyar nasara ba”.

“Koken mu shine ‘yan Nijeriya ba za su gajiya ba kan fafutukar ganin an wadatar da fannin da kuɗaɗen da yake buƙata ba”.
Ya ce, “Abu ne da ya shafi kowannen mu, don haka ya zame wajibi mu ga an yi abinda ya dace”.

Sai dai wata majiya ta bayyana cewar, Gwamnatin tarayya ba za ta cimma wancan alƙawari ba a shekara mai shigowa, domin tuni an tsara daftarin kasafin kuɗin, kafin ma gangamin shugabanni da aka gudanar a birnin Landan.

A wani ci gaban kuma, an fahimci cewar, zaman tattaunawa da ƙungiyar ta ASUU za ta yi da jami’an gwamnatin tarayya a satin da ya gabata bai tabbata ba, kasancewar gwamnati tana da wasu batutuwa da za su warware da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa. Waɗannan sun haɗa da ƙalubalolin yajin aiki da ƙungiyar likitoci ta ƙasa, da ƙungiyar ma’aikatan jinya suka jajirce a kai.