Kasafin FAAC: CBN ta buƙaci ƙananan hukumomi su gabatar da rahoton shekara biyu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kananan Hukumomi a faɗin ƙasar nan na fuskantar sabon cikas a yunƙurinsu na karɓar kason su na wata-wata kai tsaye daga Asusun Rabon Kuɗi na Tarayya (FAAC)

A halin yanzu dai ana buƙatar kowacce daga cikin ƙananan hukumomi 774 da ta bai wa Babban Bankin ƙasar (CBN) cikakken rahoto na ayyukan kuɗaɗenta na tsawon shekaru biyu a matsayin sharaɗi na tura kuɗaɗen da aka ware musu kai tsaye.

Tun a watan da ya gabata ne aka shirya fara rabon kuɗaɗen shiga kai tsaye amma sai da aka ɗage daga karshe saboda da yawa daga cikin ƙananan hukumonin sun kasa gabatar da cikakkun bayanan da ake buƙata domin sauƙaƙa biyan kuɗaɗen kai tsaye.

Kaso nasu na Naira biliyan 361.754 daga kuɗaɗen shigar da ake raba wa na Naira Tiriliyan 1.424 na wata-wata, daga baya aka raba musu ta jihohin.

Tuni dai babban bankin ya fara shirin buɗe asusun ajiya ga ƙananan hukumomin domin samun damar karɓar kason su kai tsaye daga Abuja ƙarƙashin ikon cin gashin kansu na kuɗi da Gwamnatin Tarayya ta nema musu daga Kotun ƙoli.

Kaso zai fara aiki nan da ’yan makonni kuma a nakon da ya gabata an samu shakku kan ko za su iya gabatar da rahoton tantancewar da CBN ta buƙata na tsawon shekaru biyu gabanin taron da za a yi a watan Fabrairu na kwamitin rabon kuɗaɗe na asusun tarayya (FAAC) a Abuja inda za a raba kuɗaɗen.

Majiyoyi a Babban Bankin na CBN sun shaida wa jaridar The Nation cewa bankin ba zai iya buɗe asusu na ƙananan hukumomin ba tare da cikakken fahimtar halin da suke ciki a halin yanzu.

“Ba za mu iya buɗe sabbin asusu ga ƙananan hukumomin ba lokacin da yawancinsu ba su yi aiki a matsayin wata hukuma mai zaman kanta ta gwamnati ba,” inji ɗaya daga cikin majiyoyin.

Jami’in ya ce, rahoton binciken na da muhimmanci.

Wani kwamitin ma’aikatun da ke ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya (SGF) na samar da wani tsari na aiwatar da hukuncin Kotun ƙoli kan cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Wani mamba na kwamitin ya bayyana cewa ana shirin samar da samfuri don baiwa Akanta Janar na Tarayya izini kai tsaye cire kuɗaɗen da aka ware don wasu fannoni kamar ilimin firamare, kiwon lafiya, da sauran nauyin da tsarin mulki ya rataya a wuyan ƙananan hukumomin daga cikin kuɗaɗen da FAAC ke rabawa tare da miƙa su ga hukumomin da abin ya shafa.