Kasafin kudi 2025: An ware miliyan 50 ga kowace ƙaramar hukuma don sayen taki a Kano – Hon. Massu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Shugaban kwamitin ƙananan hukumomi da sha’anin masarautu na majalisar dokokin Jihar Kano Zubairu Hamza Massu ya bayyana cewa an warewa kowace ƙaramar hukuma naira Miliyan 50 domin sayen iri a kasafin kuɗi na shekarar 2025.

Honarabul Massu wanda shi ne wakilin ƙaramar hukumar Sumaila ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan zaman majalisar.

Hamza Massu ya ce babban abin da ya fi burgeni shi ne kwakyawan tanadi da aka yi wa noma, wanda ya ce a halin da ake ciki yanzu harkar noma yana da matukar muhimmanci.

Ya ƙara da cewa “Noma ne hanya mafi sauƙi da za a kawo ƙarshen tarin matsalolin da muke fama da su na rayuwa.

“Domin a sayen iri ma kadai kowace ƙaramar hukuma an mata tanadi na Naira miliyan 50 wanda iri kawai za a saya domin neman rani da damina.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa dukkanin shugabannin ƙananan hukumomin 44 na Kano sun shigo majalisar kuma sun kare kasafin na su.