Kasar Sin ta nuna damuwa kan yadda ‘yan sandan Amurka suka kashe mutane ba bisa doka ba

Daga CMG HAUSA

Wakilin ƙasar Sin ya nuna damuwa kan yadda ‘yan sandan ƙasar Amurka suka kashe mutane ba bisa doka ba, yayin da yake tattaunawa da mai sa ido kan batun kashe mutane ba bisa doka ba, a wajen taron kwamitin kare haƙƙin dan Adam na MƊD karo na 50 jiya Laraba.

Wakilin ƙasar Sin ya nuna cewa, an sha jin labaru masu tarin yawa dangane da yadda ‘yan sandan Amurka suka ci zarafin wasu yayin da suke aiwatar da doka.

An ruwaito cewa, a cikin shekara guda bayan mutuwar George Floyd, wanda ya mutu sakamakon cin zarafi yayin da ‘yan sandan Amurka suke aiwatar da doka, masu aiwatar da doka na Amurka sun kashe ɗarurruwan ‘yan ƙananan ƙabilu a ƙasar. Haka kuma sojojin Amurka sun kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba yayin da suka gudanar da ayyukan soja a ƙetare, amma ba a gurfanar da su a gaban kotu ba.

Wakilin ƙasar Sin ya ƙalubalanci kwamitin kare hakkin dan Adam da kuma mai sa ido kan batun kashe mutane ba bisa doka ba, da su riƙa mai da hankali kan yadda ‘yan sandan Amurka suka ci zarafin wasu yayin da suke aiwatar da doka, da kuma yadda sojojin Amurka suka kashe fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba ‘yan ƙasashen waje, a ƙoƙarin ƙara azama kan gudanar da cikakken bincike kan batutuwa masu ruwa da tsaki cikin adalci da kuma gurfana da masu aikata laifin.

Fassarawa: Tasallah Yuan