Kashe Hanifa: Gwamnatin Kano ta janye shaidar gudanarwa ga makaratun kuɗi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ranar Litinin da ta gabata Gwamnatin jihar Kano ta janye duka shaidar gudanarwar da ta bai wa makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar domin sabunta su.

Kwamishinan Ilimin jihar, Malam Muhammad Sanusi-Kiru ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

Sanusi-Kiru ya nasabta ɗaukar wannan mataki da gwamnatin Kano ta yi da kashe Hanifa Abubakar, ‘yar shekara 5 kuma ɗaliba a makarantar Noble Kids Comprehensive College, wanda aka zargi mai makarantar da aikatawa.

Ya ci gaba da cewa, an janye shaidar gudanarwar ga makarantun ne don bayar da damar sabuntawa da kuma tantace masu makarantun.

A cewarsa, “Ma’aikatar Ilimi ta kafa kwamitin da zai kula da shirin yi wa makarantun kuɗi a jihar rijista.

“Ma’aikatar za ta fitar da tsare-tsare don sabunta rijistar ɗaukacin makarantu masu zaman kansu a jihar, ciki har da bi ta ƙarƙashin Ma’aikatar shari’a da Hukumar DSS da ‘yan sanda…”, da dai sauransu.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da Abdulmalik Muhammad Tanko a Kotu don fuskantar shari’a, kan tuhumar da ake yi masa da garkuwa da kuma halaka yarinya ‘yar shekara biyar, Hanifa Abubakar.