Kashi 35 na gonaki a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma sun fi ƙarfin manomanmu – Iliyasu Ishakh

Daga BABANGIDA A GORA a Kano

Da yawan gonakin manoma mazauna Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas sun gagari masu su wajen nomasu a cikin shekarun da matsalolin tsaro suke ƙara ta’azzara a Nijeriya.

Hakan ya fito ne daga bakin wani matashi mai suna Mista Iliyasu Ishak da ya ke kan gaba wajen koya wa manoma hanyoyi da dabarun noma da ma fahimtar da su sirrin tsirrai a kusan yankin Arewa a wata zantawa da manema labarai a Kano.

Ishak wanda ya ce babu abinda zai iya kawo cigaba a wannan harka ta noma face masu ruwa da tsaki su ƙoƙarta kawo ƙarshen matsalolin rashin zaman lafiya dake barazana ga talakawa da mafi yawansu suke gudanar da harkokin noma a Nijeriya.

Haka nan ma ya bayyana gwamnatoci su ƙara zage damtse wajen samar wa manoman kayan aki, kama daga hanyoyin da manoman za su rinƙa kai kayansu kasuwa idan sun noma haɗi da iri mai kyau da takin noma da sauran dukkan wasu abubuwan da manoma ke buƙata.

Matashin ya kuma ce, “lallai idan akai wannan shi ne zai iya bada damar samun cigaban da za mu iya noma abinda za mu ci har ma mu iya sayarwa a waje, kuma shi zai ƙara kawo bunƙasar tattalin arzikin da zai ƙara ɗaga darajar ƙasar mu a idon duniya.”

Kazalika masanin harkar ta noma ya ce an samu canji a wannan lokaci da manyan ‘yan kasuwa suka fara ɗaukar noma wani abu na a zo a gani a wannan ƙasa, bisa yaƙinin abu ne da mutum zai iya dogaro da shi ta hanyar wani abu da yake na dogaro da kai saɓanin shekarun baya.

“Muna ƙoƙarin samar wa manoma hanyoyin da za su taimaka masu wajen noman zamani da ƙirƙirar hanyoyin bunƙasa noma da shi kansa tsarin kasuwancin kayan noman ma matsayin mu na masana.”

Ya kuma tabbatar da tsarin da Babban Bankin Nijeriya ya fito da shi na bada tallafi wajen gudanar da noma abu ne dake matuƙar taimakawa a halin yanzu tare da kawo bunƙasar tattalin arzikin ƙasar nan ta fuskar noma da kiwo a yanzu.

Bayan nan kuma ya buƙaci matasa da su rungumi noma a matsayin sana’a da za su iya samun tagomashi na kansu kasantuwar mafi yawan ƙasashen da suka yi fice a duniya sun samu wannan ne ta fuskar noma da kiwo, inda kuma ya ce noma bai kasance batun talakawa ba ne kaɗai ko wanda ya gajiya, harka ce ta dogaro da kai.

Daga nan ya buƙaci masu ruwa da tsaki da su ƙara sa hannun jarinsu ta fuskar da noman zai samu ɗorewa a ƙasar nan, amma kuma da buƙatar gwamnati ta fara magance harkar tsaro farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *