Kashi biyu cikin ɗari ne na ‘yan gudun hijira miliyan 3.2 aka yi rajistarsu, cewar gwamnati

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Dubu tamanin da huɗu, da ɗari takwas da uku kacal, misalin kashi biyu cikin ɗari na miliyan uku da dubu ɗari biyu na ‘yan gudun hijira dake jibge a sassa daban-daban na ƙasar nan aka yi wa rajista ko hukuma ta san da zamansu, a cewar gwamnatin tarayya.

Jihar Borno ita ce akan gaba da take da tarin ‘yan gudun hijira da suka kai kimani miliyan ɗaya da dubu ɗari shida, yayin da jihar Ekiti ke biye da ita da ‘yan gudin hijira dubu biyar da ɗari uku da saba’in da bakwai.

Waɗannan bayanai sun fito ne daga bakin kwamishinan tarayya na hukumar kula da lamuran ‘yan gudun hijira, maƙaurata, da waɗanda annoba ko tashin hankali ya raba su da muhallansu, Malama Imaan Suleiman-Ibrahim, a kwanakin baya.

Ta yi waɗannan jawabai ne a taron manema labarai na 42 na fadar shugaban ƙasa da jami’an shugaban ƙasa majivanta lamuran sadarwa suka shirya a fadar Gwamnatin Tarayya dake Abuja.

Matar Suleiman ta ce, “kamar yadda ƙididdigar UNHCR ta baya-bayan nan ta bayyana, akwai ‘yan gudun hijira guda miliyan 3.2 a qasar nan waɗanda tare da UNHCR muke kula da su, yayin da muka yi wa 84,803 rajista.

“Muna da masu buƙatar mafaka guda 1,570 da fiye da 7,000 waɗanda suke jibge a biranen ƙasar nan. Mun iya dawo da ‘yan Nijeriya dake ƙasashen ƙetare guda17,334 zuwa gida, kuma a aikin kwaso ‘yan Nijeriya daga qasashen ƙetare na kwana-kwanan nan da muka yi, mun tantance guda 1,625 da suka tsere daga yaƙe-yaƙen da ƙasashen Ukraine da Rasha suke yi..”

Ta bayyana cewar, daga cikin ƙidayayyun, jihar Zamfara tana da ‘yan gudun hijira ko waɗanda tashin-tashina ya cinye gidaje ko muhallansu guda 678,000, Benuwai guda 300,000, Adamawa guda 208,334, Yobe 156,437, Neja guda 150,380, Katsina 130,113, Kuros Riba 101,404, Ebonyi 93,404, Filato guda 91,524, da Taraba mai guda 82,661.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *