Kaso mai yawa na matan da ke fuskantar cin zarafi ba su ke faɗa ba – Salamatu Bello

“Kaso saba’in bisa ɗari na mata na taimakon mazajensu a matsalolin gida”

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

Masu karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, ya ibada? Allah Ya karɓa, Ya sa mu a bayinSa da zai ‘yanta a wannan wata mai daraja. Idan ba mu manta ba, a satin da ya gabata, mun fara tattaunawa da Salamatu Bello Abdullahi, ƙwararriyar ‘yar jarida da ke gudanar da shirye-shirye masu ilimintarwa gami da nishaɗantarwa. Mun soma ne da jin tarihin rayuwarta da kuma ƙalubalen da ta fuskata a aikin jarida, sannan mun ja birki kan tambayar da muka yi mata da muka yi alƙawarin farawa da amsarta kafin wasu su biyo baya. Idan kun shirya, zan ce a sha karatu lafiya:

MANHAJA: Shin wannan lamari da ya faru bai sare ma ki gwiwa ba, har ki ka ga barin aikin jarida a matsayin mafita?

SALAMATU: Magana ta gaskiya hakan bai sare min gwiwa ba, sai dai magana ta gaskiya domin Allah a yi ta, na tsorata ƙwarai da gaske, tsoro sosai na gasken gaske, saboda idan na yi duba da cewa, tun da na taso, tsakani na da ofishin ‘yan sanda shi ne, hanya. Ita kaɗai ce ke bi da ni ta wurin in ta zamo dole kenan in bita. Duk wani abu da ke cikin ‘police station’ a labari nake jin sa. Ban tava shiga ciki ba.

To kinga a ce kwatsam sunana ya dira a CID, tsakani da Allah hanjina ya kaɗa sosai. Kafin su zo mu fara magana ne wani abu ya zo min a raina cewa, dama an ce a rayuwa akwai ƙalubale, na tuna ni ma dai dole in ci karo da nawa, wanda take na amince wannan lamari na ɗaya daga cikin nawa ƙalubalen, don haka na ɗaga hannu sama, na roƙi Allah Ya kawo min mafita, Ya sa ya zama nasara a gare ni. Dama duk wani wanda ya zama wani abu a rayuwa, ya fuskanci ƙalubalai da dama, wanda sai yana faɗa ne za ka san da su.

Da wanna ne na ji kamar an ƙara min ‘moral’ na aikina wanda watan wata rana wata ko wani zai kale ni a matsayin allon kallo don samun ƙwarin gwiwa a nasa aikin.

Waɗanne irin nasarori ki ka samu a aikin jarida?

Alhamdu lillahi, na samu nasarori da alfarma kala-kala a aikin jarida. Duk da cewa ba wani sani na aka yi ba, sai dai shi ɗan Adam ba abin wasa ba ne. Duk inda na je, in har za a samu wata ta iya gane ni, idan har aka ce ga Salamatu Bello Abdullahi, to fa gabaɗaya wurin sai ya san da na iso, wannan ni’ima ce babba. Wannan ita ce babbar nasarar da na samu a rayuwa, samun soyayyar mutane. Musamman ma mata, kasancewar shirin da nake yi ya fi tasiri a ɓangaren su, sai dai kuma shi kansa shirin ‘Shafa Labari Shuni’ bai tsaya a iya mata ba kawai, domin za ka sha mamaki idan kaga yadda maza da tsofaffi ke sauraren shirin.

Ba mu labarin yadda ki ka tsinci kanki a irin wannan aikin.

Ai idan na ba ki labarin yadda aka yi na tsincin kaina a aikin jarida sai na ba ki dariya (dariya), saboda kwata-kwata babu aikin a tsarin abinda nake sha’awa. To kinsan an ce bawa bai san inda abincinsa yake ba. A gaskiya ni ba abinda nake da buri kamar aikin asibiti. Kinsan me ke birge ni da aikin. Irin ka wanke fararen kayan nan, ka sa, kana tafiya cikin tsafta da natsuwa, ka je ka ɗauko kayan aluran nan, (dariya). Wannan tun Ina matakin firamare nake da wannan shauƙin ga aikin asibiti.

To kwatsam ba zan manta ba a shekarar 2011, lokacin an buɗa Libarty Radio, a lokacin ma tana haɗe, Turanci da Hausa, to a nan na fara aiki. A 2013 abincina ya ƙare da su, na koma Kaduna State Radio, KSMC kenan, a ƙarƙashin tashar Kada FM. Daga nan kuma rayuwa ta mayar da ni FRCM a Karama FM, a shekarar 2014, wanda har a yanzu a nan abincin yake. Alhamdu lillah.

Bari mu koma ɓangaren iyali. Kina da yara nawa?

Kamar yadda na faɗa a farko, Ina da aure, kuma Ina da ‘ya’ya biyar, sai dai a halin da nake ciki a yanzu, Allah Ya karɓi rayuwar ‘ya’yana su huɗu, guda ɗaya ne a raye, namiji, mai suna Abduljabar. Fatana ga al’ummar Annabi, su taya ni da addu’a, Allah Ya sa ya haifar min da gari da yawa, tunda masu iya magana kan ce, wai ɗa ɗaya shi ma gayya ne.

A matsayin ki ta mai gabatar da wannan shiri da ki ka ambata da ya shafi mata. Shin cin zarafin da mata ke shelanta maza na masu, wasu za ki ga har suna nuna kusan kowanne gida akwai cin zarafin matan aure, ko ya kai nauyin da mata ke ba shi?

Ƙwarai da gaske zan iya cewa akwai cin zarafi, musamman ma wannan zamani da muka tsinci kanmu a yanzu, maza suna cin zarafin mata, musamman ma kasancewar mun shiga cikin wani yanayi wanda kamar yadda Hausawa ke cewa, idan kai na da tsoka, kowa ya shafa nasa ya ji. Ke mace da aka san ki da haƙuri, ko ake kallon ki yi haƙuri a irin wannan rayuwa, to fa idan ki ka kasa jurewa da hangen nesa kan lamarin da rayuwa ta ke ciki, ki ka bijiro da wasu halayya ko dai sababi ko dama kina da su yanayi ne dai bai sa su bayyana ba, a ƙoƙarin bayyana gajin haƙuri ko rashin aminta da abinda ake yi ko ba a yi ma ki, to fa shi maigida komai zai iya yi maki a lokacin.

Sai dai a yadda na fahimci cin zarafi wanda ya amsa sunansa na cin zarafi, kaso mai yawa na matan da ake yi wa shi ba su cika fitowa su faɗi ana cin zafarin su ba, ma’ana an fi samun su cikin mata masu haƙuri. Mazan na cin zarafin su, suna ƙoƙarin dannewa. Wannan ke sa kaso mai yawa na irin waɗannan matan ba su ne ke fitowa su shelanta wa duniya cewa mazansu na cin zarafin su ba. Mafi akasanin matan da su karan kansu za su bayyana cin zarafin da ake masu za ki tarar bai taka kara ya karya ba, ko kuma ta kai tudun gajiya, ta ɗau alwashin ba zata haura ba.

Tana dai neman sanadin da za ta kai ƙaran shi ko zai zame mata hujjar da zata raba auren, wannan ke sa wani lokacin za ka iya samun har da ƙari a ababen da zata zayyano a matsayin cin zarafin da mijin ke yi mata. Wannan ke sa lokuta da dama idan irin waɗannan matan na ba ki labarin abin da miji ya masu, dole ki tausaya masu, wataƙila har ki zubar mata da hawaye. Sai dai idan da za ki tuntuɓe mijin za ki iya samun akasin hakan, kuma idan aka yi zagaye sai ki same shi da gaskiya a wasu ɓangarori.

Ita rayuwar mata da miji, bahaushe ya ce, sai Allah Ya san tsakaninsu, saboda lokuta da dama idan kin ajiye mace ta gaya maki matsalolinta da mijinta, idan ki ka zaunar da mijin ki ji ta ɓangaren sa, za ki tarar da akwai bambanci a ababen da za su faɗa. Wanda idan za ki yi hukunci da iya abinda ɗaya ya faxa kowane za ki ba shi gaskiya duba da irin abinda zai ce. Idan kuma ki ka haɗa su a tare don bin bahasi, a nan ma za ki ji wani abu daban.

Don haka ni Ina ganin irin cin zafarin da maza ke yi wa mata bai kai yadda mata ke kwarzanta shi ga duniya ba. Su dai matan da ake cin zarafin nasu, ana cin zarafin nasu, kuma suna nan suna daurewa, suna cijewa, don ba su da bakin magana, suna rufa wa mazajen nasu asiri. Idan kinga abin ya fito har duniya ta sani, to abin ya kai matakin bayyana kanshi, ba su da yadda za su iya ɓoye shi, ko kuma wasu nasu ne suka fahimce shi, suka fallasa, wanda sai bayan sun faɗa ne idan aka tilasta mata ne, sannan zata ce ai gaskiya ne. A tawa fahimta kenan.

Wacce shawara ki ke da ita ga mata ‘yan’uwanki a dunƙule?

To wannan zan iya cewa ba shawara nake da ita ga mata ‘yan’uwana ba, akwai shawarwari da dama da nake da su gare su, amma zan yi a taƙaice. Bari na fara ga mata iyaye, musamman waɗanda suka amsa sunansu a matsayin iyaye, wato matan da suke zaune a gidan mazajensu. Haƙuri, juriya, dauriya da rufin asirin da suke yi wa mazajensu a gidan aure, shi ne zai kawo zaman lafiya tsakanin su.

Ita mace wata halitta ce da Allah (S.W.A) ya ba wa daraja ta musamman, wanda da yawa daga cikin matan ba su sani ba. Mace aba ce mai mutunci, idan kin yi duba da cewa, idan ki ka fita, za a iya cewa, waccan matar aure ce, waccan kuma bata da aure. Darajar da za a ce an ba wa matar aure, ba zai zama ɗaya da wadda bata yi aure ba.

Da farko dai zan fara da waɗanda ba su da aure, duk da cewa, aure nufi ne na Ubangiji, don haka za mu fara da yi masu addu’a, Allah Ya ba su maza nagari. Sai dai zan ba su shawara su buɗe idanunsu, yayin zaɓar mazajen aure, kada su biye wa son zuciya, su zaɓi mazajen da suke hasashen sun yi wa rayuwar su tushe na ƙwarai.

Su kuma matan da suke zaune gidan mazajensu, su riƙe darajarsu kamar yadda Allah Ya ba su. Ki rufa wa mijinki asiri, ki riƙe sirrin shi, ki tsare masa gaba, ki tsare masa baya. Wallahi duk matar da ke wannan, ko mijin bai yabe ki a gaban ki ba, zai yi a bayan ki, saboda ba namijin da ba ya son mace mai wannan halayya. Ki yi haƙuri. Ita kalmar haquri ta daɗe tana yawa tun iyayenmu da kakani, abin mamaki sai ka ji wasu matan na cewa, sun yi haƙurin, amma ba su ci riba ba, to wannan zance ne kawai, domin idan ki ka ga kin yi haƙuri ba ki ci riba ba, to haɗan ki ka yi. Kalmar haquri har yau tana yawo a tsakanin mu, saboda ingancinta da amfaninta a rayuwa.

A duk lokacin da ki ka samu kanki a wani wuri, aiki ne ko kasuwanci, to fa yadda ki ka riƙe kanki, haka za a dinga kallonki. Idan kin riƙe mutuncinki, mutane za su taya ki riƙe shi ne, haka ma idan kin watsar, sai a taya ki watsarwa. Don haka Ina kira ga mata ‘yan’uwana, mu dinga haƙuri da mazajenmu, waɗanda ke da aure, waɗanda ba su su saka kyakyawan halayya a matsayin jagora yayin zaɓen mijin aure ba ƙyalƙyalin duniya ba, kuma a roƙi Allah zavi mafi alkhairi.

Sannan ta ɓangaren neman na dogaro da kai, tuni dai mata sun bazama, sun koma suna gogoriyo da maza wurin rufa wa kai asiri, don yanzu zan iya cewa, babu malalaciyar mace. Masu zuwa aiki na yi, masu sana’a na yi, don ganin sun rufa wa kansu da iyalansu asiri. Don yanzu sau da yawa za ka tarar da mace na nema ne don ta rufa wa mijinta asiri, ta hanyar ɗauke masa wasu daga cikin hidindimum gida. Kaso saba’in bisa ɗari na mata suna taimakon mazajensu, koda da kashi talatin bisa ɗari ne na lalurorin gida. Wannan kawai wata hanya ce ta gyara zaman aure, miji zai samu ƙwarin gwiwa.

A wannan gaɓa zan ja hankalin mazaje kan yaba wa matansu idan suka yi abin a yaba masu. Mu mata muna son mazanmu na yaba ƙoƙarin mu, wannan na ƙara mana ƙarfi wurin ƙari akan abinda muke yi. Duk da cewa ya kamata mu san cewa, ko miji bai yaba abinda muka yi ba, a wurin Allah muna da lada na aikatawa.

A nan zan ba wa mata shawara, ko da yabo ko ba yabo daga miji, kada ki bar wani abu da ki ke yi na kyautatawa gare shi, saboda Allah ne ake yi don shi, kuma zai ba ki lada.

Mun gode.

Ni ma na gode ƙwarai Anty Aisha, Allah Ya yi mana jagora bakiɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *