Kasuwanci da aikin gwamnati shirya wa rayuwar bayan ritaya ne – Sumayyah Sarina

Daga AMINA YUSUF ALI

Sumayyah Ibrahim Sarina ma’aikaciyar gwamnatin Jihar Kano ce sannan a lokaci guda kuma ’yar kasuwa. A tattaunarwata da Wakiliyar Manhaja, Amina Yusuf Ali, ta bayyana wa shafinmu na Kasuwanci hikimarta ta haɗa gudu da susar ɗuwawu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu so ki gabatar da kanki.
Sunana Sumayyah Ibrahim Sarina, Asalin iyayena ‘yan ƙauyen Sarina ne da ke Ƙaramar Hukumar Garko da ke nan jihar Kano. Na yi makarantar Allo, Islamiya da kuma firamare duk a cikin  ƙwaryar birnin Kano. Bayan Kammala karatun firamare ɗi na, na wuce sakandiren gwamnatin tarayya ta kwana da ke minjibir, (FGGC Minjibir). Bayan  nan, na samu nasarar Shiga makarantar koyon aikin lafiya ta ‘School of hygiene’ da ke Kano, na samu shaidar difloma. Daga nan na wuce Jamiar Bayero da ke nan Kano na yi karatun digiri na farko da na biyu a fannin kiwon lafiya (Health Education). A yanzu haka ina koyarwa a Kwalejin horar da malamai ta Sa’adatu Rimi, Sa’adatu Rimi college of Education.

Bayan aikin gwamnatin kina wata sana’a ne?
Ina sana’ar sayar da tuararurruka da kayan ƙamshi kala-kala. Yanzu ina gudanar da kamfanina mai suna Sareenah emporium. Ina sayar da su a cikin Kano, Kuma ina aikawa da su ko’ina a faɗin ƙasar nan ga masu buƙata.

Me ya ja hankalinki kika fara sana’ar turare?
Gaskiya tun tasowa ta da sana’atata na taso. Tun ban fi shekaru 8 zuwa 9 ba kakata take saro min su alewar madara, tsami gaye, mandula, albishir da sauran su.  Zuwa na makarantar kwana ya sa na watsar da sana’ar saboda rashin lokaci.  Gaskiya na taso da neman na kaina tun ban san me zan yi da ku]in ba idan na nema. Tsanar roƙo da son taimaka wa mata marasa ƙarfi ke ƙara jan hankalina da jajircewa wajen sana’ar. Duk kuwa da tarin ƙalubalen da nake fuskanta.

Kina sarar turarurruka daga wasu jihohin ko ƙasashen ƙetare, ko iyakacinki Kano?
Eh, Ina saro kayayyaki daga kasuwaninmu na nan mussaman Legas da kuma ƙashashen ƙetare kamar Dubai, Indiya, Maleshiya da Chana.

Kina da wani ko wata da kuke yin sana’ar tare, ko  wasu da suke a ƙarƙashinki da kuke yin kasuwanci tare?
Gaskiya babu wanda muke sana’ar nan tare, gashin kaina nake ci. Amma akwai waɗanda suke ƙarkashin kamfanina mata ne da ba su da karfin jari. Muna ba su kaya kan farashi,  su sayar, su samu wani abu, su kawo mana kuɗinmu, sai mu ƙara musu wasu kayan.

Ya ki ke haɗa sana’arki da aiki a tare. Kin san fa ba aiki ne mai sauƙi ba?
Ai komai da lokacinsa. Kuma dole ka tsara lokacin kasuwa, aiki da iyali yadda kowanne ba zai cutu ba. Tunda aiki na koyarwa ne, lokacin da ba ni da aji na fi posting kaya tunda kasuwancina yafi ƙarfi a yanar gizo. Kuma ina da me taimaka min wajen haɗa kayan da ake so idan bana nan. Akwai wanda kuma dole sai da kaina kamar haɗin turaruka su na fi yin su a ranakun ƙarshen mako.

Me ya hana ki dogara da aikin gwamnati kaɗai?
Ai shi kasuwanci haɗa shi da aiki yana da matuƙar amfani. Saboda kamar kana shirya wa rayuwa ko bayan ritaya ne. Lokacin da babu albashi kuma fitowar  kuɗin fanshon ma wani aiki me mai zaman kansa. Idan ya fito ɗin ma, bai taka kara ya karyan da har zai ɗauki nauyin buƙatun mutum, dana iyali ba.

Wacce nasara kike ganin kin samu a wannan harkar?
Akwai nasarori da dama da kodayaushe idan na tuna nake ƙara gode wa Allah. Domin kuwa yana daga cikin Abin alkairi a rayuwa a ce Allah ya ba ka damar ko sanya ka zama sanadin yayewa wani damuwar da yake ciki komai ƙanƙantarta. Cikin matan da muke ba wa kaya su ɗora ribarsu, in sun siyar su dawo mana da kuɗinmu, mu ƙara ba su kaya, akwai  da yawa waɗanda sanadin haka suke tsaye da ƙafafunsu, su ma suna taimaka wa wasu ma. Alhamdulillah.

Meye sirrin nasarar Sarina?
Tsai da gaskiya da amana, juriya, haƙuri da jajircewa shi ne sirrin kowacce irin sana’a. Kuma ina shawartar sauran ‘yan kasuwa ma, da su yi koyi da waɗannan halayen. 

Wanne ƙalubale kike fuskanta?
‘Yan bashi da yan mota, sai safarar kaya kaya daga wata ƙasar zuwa Nijeriya (shipping) su ne manyan ƙalubalen da na fuskanta kuma nake kan fuskanta. Wanne kira za ki yi ga mata a kan dagewa da sana’a?

mene ne kiranki ga mata?
Kirana ga mata, mu dage mu nemi na kanmu komai ƙanƙantarsa ya fi roƙo ko maula. domin su ɗin suna zubar da ƙima da mutunci musaman ga mace. Kuma suna buɗe ƙofar alfasha a bayan ƙasa.