Kasuwar hannun jari ta sake faɗuwa da biliyan N48 a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI

Harkokin kasuwanci a Nijeriya ya samu tsaiko musamman a kasuwar zuba hannun-jari ta Nigerian Exchange Limited, inda aka sake samu faɗuwa ta kimanin Naira biliyan 48 a ranar Laraba.

Adadin faɗuwar da aka samu a kasuwar ya kai kashi 0.07, wato ta rufe a tiriliyan N66.436 daga tiriliyan N66.484 kafin lokacin.

Haka ma tsarin zuba jari na ‘All-Share Index’, wanda ya faɗi da kaso 0.07, inda ya rufe da 106,090.38 daga 106,167.91 da aka samu kwana ɗaya kafin haka.

An samu faɗuwar ne sakamakon rugujewar hannun-jari a kamfanonin CONOIL da bankin UBA da sauran su.

Ratar kasuwar ya samu koma-baya ne sakamakon samun ɓangarori 32 da suka yi asara, a yayin da 19 kuma suka samu riba.

Kamfanin CONOIL ya faɗi da kaso 10 da kullewa a N331.20, yayin da Berger Paints ya faɗi da kashi 9.81 da kullewa a N18.85 a kowane hannu.

Haka ma International Energy Insurance, wanda ya faɗi da kaso 9.79 da Multiverse Mining Fell da kaso 9.66, yayin da Regency Insurance ya faɗo da kaso 8.70.

A gefe guda kuma, waɗanda suka samu riba sun haɗa da Tantaliser, wanda ya ƙaru da kashi 9.79, yayin da da Secure Electronic Technically ya samu ƙaruwar kaso 9.68.

Sauran sun haɗa da Caverton Offshore Support Group da FTN Cocoa da bankin Ja’iz da Sovereign Trust Insurance, wanda shi ya samu kaso mafi girma, da kuma bankin Zenith.