Katsina ta cika da mahalarta ɗaurin auren ‘ya’yan Sanata Lado

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Garin Katsina ya cika maƙil da manyan baƙi daga sassa daban daban na kasar nan da suka halarci ɗaurin auren ‘ya’yan jigon ɗan siyasa kuma hamshakin ɗan kasuwa, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, a masallacin Juma’a na Bani Commassie da ke Katsina.

‘Ya’yan nasa mata da aka aurar su ne Rukayya da Maryam da Fatima da Dakta Zainab Yakubu Lado waɗanda hamshakin ɗan kasuwa Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal ya kasance waliyyinsu a madadin Sanata Lado.

Aurarrakin sune na Rukayya Yakubu Lado da angonta Abubakar Zaharaddeen wanda tsohon babban hafsan sojin sama, Air Vice Marshall Sadiq Abubakar, ya karɓar masa auren da kuma Fatima Yakubu Lado da angonta Khalid Kabir Barkiya wanda mahaifinsa Sen. Kabir Barkiya ya amsar masa auren.

Hakazalika, an ɗaura auren Dakta Zainab Yakubu Lado da Farfesa Wasiju Madina Almustafa wanda Gwamna Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya amsar masa auren.

Ta huɗun ita ce Sabira Yakubu Lado da angonta Aminu Abubakar Musa wanda Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya zama wakilinsa a amsar auren.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ne ya tarbi manyan baƙin Kuma ya raka su zuwa wurin ɗaurin auren tare da sauran manyan baƙi da suka haɗa da ‘yan majalisar tarayya da na jiha da hakimai da sauran masu riƙe da sarautun gargajiya da manyan ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar.

Ɗaurin auren ya kuma samu halartar ‘ya’yan jam’iyyar PDP daga dukkan mazaɓun Jihar Katsina 361, har ma da jiga-jigan jam’iyyar da dama, cikinsu har da tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Mustafa Inuwa.

Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Katsina, Sheik Yakubu Musa Hassan, shi ya jagoranci addu’o’in samun zaman lafiya ga anguna da amaren, tare da addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Yakubu Lado dai tsohon Sanata ne, tsohon ɗan majalisar wakilai, tsohon mamba a hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC), tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ƙanƙara kuma tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina karo uku.

Ya kuma yi fice wajen tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi, da mata, da matasa, da ɗalibai, da ‘yan gudun hijira, da gajiyayyu, da zaurawa, da marayu, da marasa galihu, da ‘yan siyasa a dukkan matakai.