Kawar da rashin tabbaci a duniya ta hanyar kyakkyawar hulɗar Sin da EU

Daga CMG HAUSA

Da yammacin ranar 1 ga watan Afrilu, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar ƙungiyar tarayyar Turai Charles Michel, da shugabar hukumar gudanarwar EU, Ursula von der Leyen, ta kafar bidiyo a Beijing.

Inda shugaba Xi ya yi tsokaci cewa, “Kamata ya yi Sin da ƙungiyar tarayyar Turai EU, su kasance a matsayin wasu manyan ginshikai biyu wajen tabbatar zaman lafiyar duniya, da kuma kai dauki kan yanayin rashin tabbaci na halin da duniya ke ciki ta hanyar kyakkyawar hulɗar dake tsakanin Sin da EU.”

Wannan shi ne batu na gaskiya, da kuma tattaunawa mai zurfi tsakanin shugabannin Sin da EU. Ɓangarorin biyu ba kawai suna son zurfafa kyakkyawar fahimtar dake tsakaninsu ba ne, har ma sun cimman matsaya kan muhimman batutuwa da dama, lamarin da ke isar da wani muhimmin sako ga duniya dake nuna buƙatar yin hadin gwiwa da juna don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya. A daidai lokacin da annobar cutar COVID-19 da rikice-rikicen shiyyoyi ke ci gaba da bazuwa, wadannan sakonni suna da muhimmanci kuma suna da matuƙar tasiri wajen kawar da rashin tabbaci din da duniya ke fuskanta.

Mai fassarawa: Ahmad daga CMG Hausa