Kebbi: Mutanen da sanƙarau ta halaka sun kai 56

Daga BELLO A. BABAJI

Ɓarkewar cutar sanƙarau, wadda a turance ake kira da ‘cerebrospinal meningitis’, ta yi sanadin mutuwar kimanin mutane 56 a ƙananan hukumomi uku dake Jihar Kebbi.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Alhaji Yunusa Musa Isma’ila, wanda Babban Sakataren Ma’aikatar, Dakta Shehu Nuhu Koko ya wakilce shi, ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi, ranar Laraba.

A yayin ganawar, an samu wakilci daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Asusun Tallafa wa Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da kuma ‘Medecins Sans Frontieres’ (MSF).

Kwamishinan ya ce, sun samu rahoto daga ofishin kula da lafiyar al’umma game da mutanen da aka kawo masu ɗauke da alamun zazzaɓi, ciwon kai mai tsanani, riƙewar wuya, amai, kasala da sauransu, waɗanda a wasu lokutan ke haddasa mace-mace.

Ya ce, ganin haka ya sa aka gaggauta ɗaukar samfuri tare da aika wa zauren bincike na ƙasa dake Abuja domin tabbatar da ɓarkewar cutar.

Kamar haka ne aka gudanar a Cibiyoyin Lafiya na Ƙananan Hukumomin Aliero, Jega da kuma Gwandu, waɗanda su ne abin ya shafa.

Ya ƙara da cewa, sun samu rahoton kesakesai guda 653, inda suka aika da 17 Abuja, waɗanda daga ciki aka samu biyar ba sa ɗauke da cutar yayin da biyar kuma suna ɗauke da ita.

Kwamishina Musa Isma’ila ya kuma ce, sun samu maganin riga-kafin cutar guda 3,000 daga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, waɗanda suka raba wa ƙananan hukumomi ukun.

A Aliero an samu kesakesai guda 1,550 waɗanda daga ciki akwai wasu daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jihar da aka yi wa riga-kafi, yayin da aka yi wa 798 a Gwandu, sai kuma 450 a Jega.

Kazalika, ya ce gwamantin jihar ta fitar da Naira miliyan 30 domin sayen magunguna da wasu ababen da ake buƙata domin daƙile yaɗuwar cutar acikin al’umma, waɗanda tuni aka raba wa ƙananan hukumomin su.