Kefas ya cinye zaɓen Taraba

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ayyana Kefas Agbu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Jihar Taraba.

A cewar INEC, Agbu ya lashe zaɓen ne bayan da ya kere wa takwarorinsa da yawan ƙuri’u 257,926.

Hukuma ta ƙara da cewa, ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Muhammad Yahaya shi ne ya zo na biyu da ƙuri’u 202,277.

Yayin da Emmanuel Bwacha na jam’iyyar APC ya zo ma uku da ƙuri’u 142,502 kamar yadda Naturen zaɓen, Farfesa M.A. Abdulazeez ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *