Kifin ƙanƙara: Gwamnati ta ba mu lambar yabo kan tsaftar sana’armu – Sani Lawan Sani

Daga BABANGIDA GORA a Kano

Sana’ar kifi mai ƙanƙara sana’a ce da ma fi akasari ba Hausawa ne suke gudanar da ita ba a da, amma a yanzu Hausawa sun yi mata kaka-gida. Wakilin Blueprint Manhaja, Babangida Gora, ya samu zantawa da shugaban ƙungiyar masu sayar da kifi mai ƙanƙara na Jihar Kano, Alhaji Sani Lawan Sani. Ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.

MANHAJA: Da farko, masu karatu za su so su san waye Alhaji Sani Lawan?
SANI: To kamar dai yadda ka faɗa, sunana Alhaji Sani Lawal Sani, kuma ni ne shugaban masu sana’ar sayar da kifi mai kankara dake nan bayan dogon banki da ke Titin Zariya a Jahar Kano.

Ko za ka iya bayyana mana yadda ita kanta sana’ar sayar da kifi mai ƙanƙara ta ke?
Ita wannan sana’a ta kifi mai ƙanƙara sana’a ce wadda za mu iya cewa a lokutan baya ba a ƙasar Hausa take ba. Hasali ma Yarabawa ne suka zo mana da ita, amma yau ga shi yaran gidansu ne suka juya ya zuwa iyayen gida. Dalili kuwa shi ne, lokacin muka fara ta, Yarabawa ne suke kawo kifin daga ƙasashen ƙetare, mu kuma mu yi musu aiki don samun dogaro da kai. Amma yanzu kusan mu ne muke jan ragamar kasuwancin gabaɗaya. Haka kuma kusan da an fi sanin nau’in kifi kamar su sukumbiya da tarwaɗa, amma zuwan kifi mai ƙanƙara a halin yanzu ya ƙara sa kasuwar tana ƙara gaba. Sannan ka san Kuma akwai nau’inkan kifi ya fi kala ɗari kama daga kuroka, sukumbiya fako, sabalo, sadin, shawa da tuna da dai sauransu.

Kasancewar wannan kifi mai ƙanƙara daga ƙasashen ƙetare ake shigo da shi, za mu iya sanin hanyoyin da kuke bi domin shigo da su?
Kusan kamar yadda kace ba anan ƙasar ake samar da shi ba, haka ne wannan. Shigo da wannan kifi kamar shigo da mai ne ko fitar da shi zuwa wata ƙasa. Don haka ne wasu lokutan za ka ji gwamnati ta ce ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen shigo da kifi. Haka kuma shi ma kifi lasisi ake badawa kamar sauran kayan da ake shigowa da su ta ruwa daga jihohin da suke da ruwa kama daga Fatakwal, Warri ko Legas, to daga nan ne mutanenmu za su je waɗannan jihohi don su saro su kawo zuwa jahohinmu na nan.

Ko ku ma kuna kiwo ko noman kifi a nan?
Eh,to gaskiya mu a nan ba mu noma irin waɗannan kifin mai ƙanƙara, saboda ba zai iya rayuwa a nan ba. Kusan irin wanda muke nomawa a nan shi ne karfasa ko  tarwaɗa. Kuma ita ma ba ko’ina ba, ta fi yawa a kudanci ƙasarmu. Amma kuma zan iya cewa akwai ruwan da idan ka jefa wani kifin ba zai iya rayuwa ba.

Wanne hoɓɓasa kuka yi wajen ganin kun rage zaman kashe wando a tsakanin matasan Nijeriya?
Da ma kasuwar ta matasa ce kai tsaye ma. Saboda haka, idan ka zagaya kusan wannan kasuwa tamu za ka ga duk yawanci matasa ne, manyan ƙalilan ne. Duk da cewa mun yi karatu bakin gwargwado, amma mun fi mai da hankali ga wannan sana’a. Muna ɗaukar kifi mu ba wa matasanmu su ɗauki kifin su shiga cikin gari su sayar, su samu abinda za su dogara da kansu. Idan da da safiya ka zo nan ma, to kafin ka shigo nan sai ka yi da gaske, kasancewar yawan matasan dake zuwa ɗaukar kifin. Kuma da wannan muke rage wa gwamnati matasan da ba su da aikin yi. Ka san rashin aiki ko sana’a ga matashi ba ƙaramar illa ba ce. Ko ka same shi yana shaye-shaye, ko ɗauke-ɗauke, ko wani abinda zai kawo rashin kwanciyar hankali ga al’ummarmu. Sama masa abin yi ne zai ɗauke masa hankali. Idan ya ɗauki tallan kifin, har yakan manta ma da wasu abokai ko makamantansu.

Yaya dangantakar ƙungiyarku take da gwamnati?
Za mu iya cewa “danjuma ne da danjummai”. Domin kuwa mu da ma ƙarƙashin ma’aikatar kula da kasuwanci muke, kowa ya san wannan. Don kuwa akwai kyakkyawar fahimta da gwamnati da take ba mu damar faɗin dukkan buqatunmu tare da ba mu shawarwari tare da faɗa mana idan gyara ya taso, don mu gyara. Idan ka duba ma nan za ka ga Kwamishinan muhali har lambar yabo ya ba mu sakamakon mai da hankali wajen tsabtace masana’antarmu,a maimakon a kama mu da laifi, amma ka ga sai san barka.

Za mu so mu ji ƙiyasin yawan mutanen da suke gudanar da wannan sana’a?
Waɗanda suke da rajista a wajenmu, sun wuce  mutum dubu goma a halin yanzu. Haka wasu daga nan idan sun ɗauka, suna da yaran da suke ba su, su shiga gari. Ka ga su waɗannan ba mu sa su ma a lissafi ba.

Waɗanne nasarori ka samu a cikin shekaru uku da ka shafe a kan wannan kujera ta shugabancin ƙungiyar?
Nasara ta farko zan iya cewa ita ce, yadda muka ja matasa a jiki tare da sama musu sana’ar dogaro da kai. Sai batun tsabtace masana’antarmu da a baya idan mutane za su wuce ta nan sai sun toshe hancinsu. Yanzu kuwa sai ma mutum ya wuce yana leƙen me ake yi a nan. Haka Kuma akwai batun zamantakewa ta kirki da zaman lafiya tare da aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnati. Sannan a tsaye muke don ganin an magance matsalolin da  za su iya tasowa  a kodayaushe da dai sauransu.

Mece ce buƙatarku ga Gwamnati? 
Alhaji Sani: Kusan koyaushe buƙatarmu ga gwamnati bai wuce roƙon sama mana guri na din-din-din da mu ma za mu samar da dukkan abin da muke buƙata. Domin idan ka dubi wannan guri, sai dai a ɗan zauna kawai, ba don ya wadatar da mu ba.

Waɗanne ƙalubale ku ke fuskanta?
A lokutan baya mun sha fama da matsalar wutar lantarki. Amma zuwana wannan kujera, mun yi duk mai yiwuwa, kuma mun yi nasara tsakaninmu da kamfanin wutar lantarki. Kuma ya zuwa yanzu ta zama tarihi. Sai matsala ta biyu, batun gurin din-din-din da muke fatan gwamnati na bakin ƙoƙarinta don sama mana.

Daga ƙarshe, wanne saƙo ka ke so ka isar?
Gaskiya akwai godiya ga Kwamishinan muhalli da nake son isarwa bisa yadda su ke sauraronmu tare da ba mu shawarwari kan abinda ya shige  mana duhu. Hakazalika, godiya ta musamman ga Khadimul Islam watau, Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda yake kula da mu. Sannan muna miqa godiyarmu ga abokan sana’armu, tare da ba su haƙuri wajen ƙara samar da cigaba mai ɗorewa dan bunƙasar kasuwancinmu.

Mun gode.
Mu ma mun gode.