Daga ƊANLADI Z. HARUNA
Kasuwanci, musamman na yanar gizo, yana tattare da kasada da ganganci da kuma tarangahuma. Wasu ma sun ce kasuwancin intanet tamkar cinikin biri a sama ne. Don haka masu bincike suke ɗora nazarinsu akan cewa kasuwancin intanet ya sha bambam da na zahiri. Domin shi a mafi yawan lokuta, daji ne da ba shi da ƙyaure.
Kowacce irin harkar intanet na ɗauke da wasu alamu da a zahiri ana iya alaƙanta su da damfara ko rashin tabbas. Ta haka idan an samu matsala, ana shan wahala kafin a warware ta. Wannan kenan.
Bayyanar MTFE, ya zo da sabon salo wanda a ba aya babu irinsa na gudanar da hada-hadarsa. Wannan ta sa ake ta waɗari tsakanin ƙwararru da masu zuba dukiyarsu a ciki, inda ƙwararrun ke masa kallon ta gina ba ta shiga ba.
A nawa nazarin, abubuwan da ƙwararrun ke faɗa na iya zama daidai amma fa ba zai yi tasiri a harkokin da MTFE ke yi ba. Bari mu duba wasu daga ciki.
Na farko, qwararrun suka ce, kamfanin ba shi da sanayya saboda ba a san wanda ya kafa shi ba. Wannan iƙirarin ba daidai ba ne. A rubutana na baya, na bayyana wadanda suka yi hamasar gina kamfanin. Kuma ban fada haka da ka ba, sai da na yi nawa nazarin kuma na amince da sakamakon da na samu.
Har ila yau kuma, a duniyar Kirifto, sanin jagororin kamfani ba shi da muhimmanci, illa iyaka dai aikinka ya bayyana ko kai wane ne, watau abin da ake kira ‘PoW’ da ‘PoS’ a karkarshin kulawar ‘pseudonymous addresses’. Babban abin da ya sa ƙwararrun masu nazari ke damuwa da sanin suna ko tarihin masu kamfani shi ne abin da ake kira ‘Managemet Risk Analysis’, wanda wajibi ne ga dukkan mai nazarin kamfani domin sanin inda alkiblar mamallakansa suka sa gaba.
Sai dai a duniyar Kirifto an fi damuwa da ‘Failure Mode and Effects Analysis (FMEA). Watau in dai za a samu karuwa ko ta kwana guda ce, to ana iya ganganci a shiga a fita kafin komai ya rufta.
Yawancin kamfanonin Kirifto na boye sunayensu ne saboda gudun kamun kazar kuku daga kasar Amurka da sauran kasashe kamar China da sauransu. Saboda a irin wadannan manyan giwayen, idan suka bushi iska kawai sai su datse kamfanin kirifto da sunan ya karya doka, to da ma kasuwanci ne da ke bisa iska, nan da nan sai ka ji ya durkushe.
Wannan ta sa kwanaki da kyar XRP ya tsira da taimakon kotu. Haka kuma Binance, duk karfinsa da ban gaskiyar da aka ba shi a duniyar kirifto bai yarda da Amurka ba. Don haka ba za ka zargi MTFE don sun qi yarda su shiga ƙasar da za a daka musu wawa ba.
Mun ga yadda ta kaya da Liberty Reserve da Mega Upload da sauran kamfanonin da suka bayyana sunayen shugabanninsu da yadda aka kwace dukiyar masu zuba hannun jari ta zama karkashin lalitar Amurka babu kunya babu tsoro.
Na gaba, qwararrun suka ce MTFE na tafiya ne akan Ponzi. Scheme watau ɗaukar kudin mutane suna biyan wasu. Ko kuma wanda yake ciki shi zai ɗauki wani ya biyo ta karkashinsa da zai rika samun wani kaso daga abin da mutum ya saka. Wanann haka yake.
To amma inda gizo ke sakar shi ne, a tsarin harkar intanet, Referral Program wajibi ne, domin kuwa yawan mutane shi ne kasuwa. Ita intanet ba kamar kasuwar zahiri take ba. Idan kamfani ko mutum ya yi nasarar tara mabiya, to suna iya zame masa jari. Shi yasa kowa ke fafutukar tara mabiya a social media da sauran wurare. Duk kasuwancin da ba shi da dumbin mabiya to zai yi asarar substantial revenue.
Dauki misali da Thread na Mark Zukabag, wanda a satin farko ya samu mabiya kusan miliyan 100, amma cikin ƙanƙanin lokaci da ya rasa fiye da rabinsu nawa aka ce sun yi asara? An ce sama dala biliyan daya!
Don haka mutane su ne jarin kowanne kamfani a intanet. Inda MTFE suka bambanta da sauran shi ne, ba sa rowar hana mutanen da suka yi kokari suka jawo musu mabiya har suka zuba dukiyarsu. Suna bulguta musu wani abu. Ba kamar sauran wurare irin su Pi Network da su Ink Nation da suka bar mutane cikin igiyar zato ba.
Abu na biyu cikin wannan kuma shi ne, shi Ponzi Scheme ba dukkaninsa ba ne abu mara kyau ba. Har yanzu ana ta gwama numfashi akan MLM da Pyramid Scheme da kuma Referral Program. Dukkan waɗannan, wasu bigire ne a cikin Ponzi, wanda a yanzu duka an amince da cewar referral program abu ne mai kyau.
Har ma an gindaya wasu sharuɗɗa da matakai da kowane kamfani zai bi idan yana so yayi nasara. Daya daga cikin matakan shi ne raba riba ga waɗanda suka kawo maka abokan ciniki. Mu a hausa muna kiransa la’ada ko ladan ganin ido ko kuɗin takalmi da sauransu.
To ka ga kenan MTFE da ke rabawa mutane ladan gave ba za a ce sun yi laifi ba.
Abu na gaba. MTFE halastaccen kasuwanci ne?
Zan dora nan gaba.