Kiris ya rage Obasanjo ya yi mini ritaya daga aiki – Buratai

Daga UMAR M. GOMBE

Tsohon shugaban rundunar sojan Nijeriya, Lt. Gen. Tukur Buratai, ya bayyana cewa, kiris ya rage tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi masa ritaya daga aikin soja shekaru 21 da suka gabata. Ya ce, wannan ya faru ne a lokacin yana matsayin Manjo, tare da bayyana samun zarafin kaiwa matsayin ‘Lieutenant General’ da kuma Babban Hafsan Hafsoshi da ya yi a matsayin al’amari da ya shiga tarihi.

Buratai, ya yi wadannan bayanan ne yayin da yake jawabin bankwana wajen mika ragamar aiki ga magajinsa Maj. Gen. Ibrahim Attahiru a babban ofishin sojoji da ke Abuja a wannan makon.

A cewarsa, “Kadan ya rage tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi mini ritaya daga aiki shekaru 21 da suka wuce.

“Murabus da na yi bayan shekaru 40 a bakin aiki ya kafa tarihi, kuma abin godiya ne.”

Yana mai cewa, aikin sojan Nijeriya ba zai taba zama yadda al’amarin yake ba sa’ilin da yake jagorancin fannin duba da irin nasarorin da bangaren ya samu a karkashinsa kafin ya yi murabus.

Haka nan ya ce, “An samu daidaito a sha’anin sojojin Nijeriya a karkashin jagaorancina, kama daga inganta dabarun tattara bayanan sirri da samar da ingantattun kayayyakin aiki zuwa samun daidaito a sha’anin tsaron kasa.”

Ya jaddada cewa, za a rinka tunawa da zamanin jagorancinsa saboda irin ayyukan cigaban da sojoji suka samu a karkashinsa, da suka hada da kyautata yanayin aiki, inganta albashin sosjoji da sauransu.

A nasa bangaren, sabon shugaban rundunar, Maj. Gen. Ibrahim Attahiru, ya yi kira ga daukacin sojojin Nijeriya da su bada hadin kansu wajen ci gaba da ingata aikin soja.