Kisan ƙare dangi Isra’ila ke yi a Gaza – Yariman Saudiyya

Daga BELLO A. BABAJI

Yariman ƙasar Saudiyya mai jiran gado, Muhammad bin Salman ya yi alla-wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza, inda ya kwatanta hakan da ‘kisan kare dangi’.

Ana ganin wannan dai shi ne suka mafi zafi da wani jami’in gwamnatin Saudiyya ya yi tun fara yaƙin na Gaza a shekarar da ta gabata.

Da ya ke magana a taron ƙoli na ƙasashen Musulmai da Larabawa, Yariman ya soki Isra’ila kan hare-haren da ta kai a ƙasashen Lebanon da Iran.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, Isra’ilar ta musanta cewa dakarunta na aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a Gaza.

A wani mataki na kyautata alaƙa tsakanin Riyadh da Tehran bayan zaman tankiya a baya, Yarima Bin Salman ya gargaɗi Isra’ila kan ƙaddamar da hare-hare a Iran.

Wasu shugabanni sun bi sahun mutumin da ake wa kallo a matsayin shugaban Saudiyya wajen yin kira ga Isra’ila da ta janye baki-ɗaya daga gaɓar Yamma da kuma Gaza.

A ɗaya gafen, ministan harkokin wajen Saudiyya ya ce “gazawar al’ummomin ƙasashen waje” ne cewa ba a dakatar da yaƙin Gaza ba, inda ya zargi Isra’ila da haddasa yunwa a faɗin yankin.