Kisan gilla ga Hanifa ya girgiza ƙasa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Na daɗe ban ga labari mai ban tausayi ko takaici da ya girgiza dukkan jama’a kamar irin kisan gilla ga ƙanƙanuwar yarinya ’yar shekara 5 kacal mai suna Hanifa da shugaban makarantar da ta ke karatu ‘NOBLE KIDS’ a Kano, Abdulmalik Tanko ya aikata ba.

Ko daga taken wannan rubutu da ya kawo ‘GIRGIZA’ akwai nuna damuwa da kukan zuci a wannan lamarin. An san dai girgizar ƙasa kan ruguza gidaje da sanya koguna su tumbatsa har a samu ambaliyar ruwa har ma ya kai ga rasa rayuka. Hakanan shi wannan labari ya girgiza zukatan mutane ya sanya rashin barci ga idanu da dama, ya sanya mutane ƙara addu’ar neman taimakon Allah don rabuwa da miyagun iri da ba su da ɗigon imani ko ƙwayar zarra a zuciyarsu. Wani babban abin damuwa shi ne yadda wannan abin takaicin ya fito daga mutum mai sunan malamin makaranta da aka ba wa amanar riƙon yara. Ba ma riƙon yara ba, har koya musu tarbiyya da kare su daga dukkan wata damuwa da tabbatar da cewa bayan an tashi daga makaranta an ɗauki yara an mayar da su gida lafiya.

A zamanin baya ma malami kan je har gida don bincika lafiyar ɗalibi ko ɗaliba in an ga ba su zo makaranta ba. Duk wanda ya yi karatu a shekarun samun ’yancin Nijeriya har zuwa shekarun 1980 zai ba da shaidar malaman kan iya zama tamkar iyaye ko ma fiye da iyayen a wajen kula da yara. A zamanin in mutum ya tura ɗansa makaranta hankalinsa a kwance ya ke don ya san ɗan na hannu mafi kyau daga zaman yaro a gida. Alaƙar iyaye da malaman makaranta kan zama kamar ta ɗan uwa ne na jini mai sanin zumunci da ƙarfafa zaman tare da gadon iyaye da kakanni.

Farkon labarin ya nuna malamin ya na daga cikin sahun farko da su ka garzaya don jajanta wa iyayen marigayiya Hanifa yana mai sharɓar kuka alhali shi ya sace marigayiyar. Nan take hakan ya tuna min da labarin sarkin munafukai a zamanin Manzon Allah mai tsira da aminci wato Abdullahi bin Ubaiyi bin Salul wanda hawaye kan kwarara daga idanun sa tamkar mai tsananin Imani alhali Musa ne a fuska Fir’auna a zuci. Irin waɗannan mutanen ba a gano su da suffar jikinsu ko fuskarsu, amma sai sun aikata wani aiki ko sun yi wata muguwar magana a kan gane matsayar su ta marar sa imani ko mutunci.

Ga waɗanda ba su samu cikekken labarin nan mai ban tausayi ba, rundunar ’yan sanda a Kano ta cafke shugaban wata makaranta mai zaman kan ta ‘NOBLE KIDS’ mai suna Abdulmalik Tanko don sacewa da kashe ɗalibarsa Hanifa Abubakar mai shekaru 5.

Binciken ’yan sanda ya gano cewa malamin tun farko shi ya sace ɗalibar ta sa inda ya kai ta gidan sa da neman kuɗin fansa Naira miliyan 6. Bayan cafke shi, Tanko da kansa ya shaidawa ’yan sanda cewa Hanifa ta gane shi don haka ya shayar da ita guba ta maganin kashe ɓeraye ta mutu sannan ya sa wani mai suna Hashim Isyaku ya taya shi aikin kai ta harabar makarantarsu inda aka bunne ta.

Majiya daga gidan su yarinyar ta bayyana cewa, malamin na daga mutanen farko da su ka zo su ka jajanta mu su kan sace Hanifa ya na mai zubar da hawaye.

Tuni an tono Hanifa aka kai ta asibiti inda likita ya tabbatar rai ya yi halin sa daga nan a ka miƙa ta wajen iyayen ta don jana’iza bisa tanadin Islama. Bayan kammala bincike za a gurfanar Tanko gaban kotu.

Tamkar amsa kiraye-kiraye ɗimbin jama’a, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ba da tabbacin jinin yarinya mai shekaru 5 Hanifa da malamin makarantar su Abdulmalik Tanko ya yi wa kisan gilla, ba zai tafi haka kawai ba. A matakin farko ma gwamnatin Kano ta rufe makarantar da mugun malamin ke jagorantar wato ‘NOBLE KIDS’ don gudanar binciken kwakwaf.

Kwamishinan labaru na jihar Muhammad Garba ya ba da sanarwar cewa lalle gwamnati za ta tabbatar an hukunta wanda ya yi kisan.

Malamin Abdulmalik Tanko wanda ya sace Hanifa ya karɓi kuɗin fansa sannan ya kashe ta, ta hanyar sanya ma ta guba, ya na hannun ’yan sanda inda bayan kammala bincike za a gurfanar da shi gaban kotu tare da abokan mugun aikinsa. Kisan gilla ga Hanifa ya jawo matuqar takaici da ɓacin rai tsakanin dukkan ’yan Nijeriya inda aka yi ta yada hotunan ’yar yarinyar da miqa ta’aziyya. Wasu ma sun samu ’yan gajerun faya-fayan bidiyon yarinyar mai ƙoƙarin karatu lokacin tana raye. Hakanan ga mai matuƙar qwarin zuciya wasu sun yaɗa faifan bidiyon yadda aka tono Hanifa don yi ma ta sutura ta hanyar da ta dace. Har lokacin da na ke rubutun nan, ban iya daurewa na kalli faifan nan na tono gawar Hanifa ba.

Kallon irin wannan faifan ga mutane masu irin zuciya ta, zai sanya ɗaukar dogon zamani cikin juyayi da rasa samun sukuni na gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda aka saba. Na ga wasu ma na ƙara taya zaman makokin marigayiyar ta hanyar sanya hoton ta a madadin hotunan shafukan sun a yanar gizo da addu’ar Allah ya sa mai ceto ce ya kuma ba wa iyayen ta haƙurin jure wannan rashin. Na wasu sun yi dogayen rubuce-rubuce na jan hankalin hukumomi don ɗaukar matakan da su ka dace na yaqi da ɓullowar miyagun laifuka a tsakiyar al’ummar da a baya samun faruwar hakan sai dai a tatsuniya ko a cikin shirin silima.

Da farko da yawa mutane ba su tayar da hankalin a kan sace Hanifa ba, tun da an yi maganar kuɗin fansa da ya nuna in an biya yarinya za ta dawo gida kamar wasu da dama su ka samu dawowa a wannan ƙalubale da ya zama ruwan dare game duniya a yankin arewa maso yamma da jihar Neja a arewa ta tsakiya. Tashin hankalin ya tsananta bayan labarin kisan gilla ga yarinyar da hakan ma ya kasance a hannun malamin ta da aka damƙa ma sa amana kuma har ma ya zo ya jajanta alhali yarinya na hannunsa.

Wani abun lura satar ba ta irin ’yan bindiga ba ne masu fitowa kan manyan tituna riƙe da bindigogi su sace mutane su kuma shige da su daji ko kuma su shiga ƙauye su kashe na kashewa su sace na sacewa; wannan ya zo daga ɓarawon zamba cikin aminci kuma daga cibiya mai daraja wato makaranta. Ka ga mugun aikin ya fito ne daga inda ba a tsammani, a na zaton wuta a maƙera sai a ka same ta a masaƙa. Hakanan ma saɓanin ɓarayin daji da ba su damu da a ka gane su ba tun da sun riga sun aiyana kan su a matsayin ɓarayin, shi dai Abdulmalik Tanko ya damu ne da cewa yarinya mai basira ta shaida shi don haka bayan saƙo ta za ta iya tona ma sa asiri a wajen iyayen ta.

Zullumin tonon asirin duniya yasa ya shayar da yarinya guba ta rasa ran ta. Cikin ikon Allah wannan bai sa mugun mutumin ya samu rufin asirin ba tun da an cafke shi. Haƙiƙa ko Tanko bai gamu da hukuncin da ya dace a duniya ba zai gamu da hukunci a ranar gobe kiyama. Tanko ya ɗauka ne zai hallaka yarinya sannan ya sha shagalin sa da miliyoyin Naira na kuɗin fansa? Hakan dai bai yiwu ba, kuma hakan ya ƙara buɗe idanun jama’a cewa a zamanin yau ba a gane na ƙwarai daga wajen da ya ke aiki ko irin suffar jikinsa.

Fatar da masu nazari ke yi ita ce a zurfafa bincike don yiwuwar gano wasu asirai na Tanko da wataƙila ya aikata a baya ba tare da an gano shi ba. Ta kan yiwu ya tava aikata irin wannan mugun aikin ko taimakawa wasu abokan burinsa wajen miyagun aiyuka don samun kuɗi ta mummunar hanya. Kama Tanko zai sa wasu iyaye da irin haka ya taba samun su, za su buƙaci a gudanar da bincike don gano gaskiya. Kimanin shekaru biyu da su ka wuce an gano wasu yara da a ka sace daga Kano a ka kai su kudanci inda aka sayar da su. Bayan nan ma an gano wasu yaran a kudu da a ka sato daga Gombe. Ga labaru nan birjik da ke nuna yadda rayuwar yaran mu ke cikin hatsarin faɗawa hannun miyagun iri da su ka zavi neman kuɗi ta hanyar haram ko kuma ta hanyar ko a mutu ko a yi rai.

Ni dai ina ba da shawara ga dukkan iyaye su riƙa yi wa yara addu’a kafin tafiya makaranta ko fita waje zuwa anguwa. Masu yin addu’ar kuma su ƙara dagewa don hakan na taimakawa ainun. Sannan a riƙa yin sadaka don neman rahamar Allah.

Hukumomi kuma a nan su yi tsayin dakan tabbatar da hukunta masu aikata miyagun laifuka don gani ga wane ya ishe wane jin tsoron Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *