- Ya ce kare kai halas ne a doka
Daga BASHIR ISAH
Wakilin Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a Majalisar Wakil ta Ƙasa, Hon. Dachung Musa Bagos, ya yi kira ga jama’ar yankinsa da su tashi su kare kansu daga kashe-kashe da haren-haren da ake kai musu.
Ɗan majalisar ya ce kare kai abu ne da doka ta yarda da shi.
Bagos ya nuna baƙin cikinsa kan sabbin hare-haren da aka kai a yankunan Mangu da Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a ranakun Asabar da Lahadin da suka gabata, inda aka kashe sama da mutane 20.
Daga nan, ɗan siyasar ya yi kira ga ‘yan Nijeriya musamman mazauna ƙauyukan Filato da lamarin ya shafa da su miƙe su kare kansu daga hare-haren da suke fuskanta.
Ya ce, “Abin baƙin ciki, ana kai hare-hare da kashe ‘yan ƙasar da ba su ji ba, ba su gani ba kulli yaumi a Jihar Filato, musamman kuma a yankunan Riyom, Barkin Ladi da Mangu.
“Duk da cewa tun a watan Mayun 2023 an kashe ɗaruruwan rayuka, kuma mazauna karkara ba sa iya tafiya gona.
“Akwai sansanonin da dama na waɗanda suka rasa matugunnansu, an karɓe musu filaye an kuma lalata gonaki.
“A ranar Asabar aka kashe wasu mutum 12 a Mangu, haka ma ranar Lahadi da daddare an kashe wasu masu haƙar ma’adinai bakwai a mazaɓata. Wannan abin baƙin ciki ne, anin tir kuma dabbanci,” in ji Bagos.