Kisan kai: Yadda sakin ɗan gidan tsohon Sbugaban Ƙasa, Aminu Yar’Adua daga kurkuku ya tayar da ƙura a Adamawa

Bayanai daga jihar Adamawa na nuni da cewa hankula sun tattashi sakamakon sake ɗan gidan tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Musa Yar’Adua, wato Aminu Yar’Adua, da kotun Majastare ta yi daga kurkuku a ɓoye wanda ake zargi da laifin kisa

An gurfanar da Aminu Yar’Adua a kotu ne bisa tuhumar kashe wasu mutum huɗu da mota a Adamawa sakamakon gudun wuce misali da mota.

‘Yan jihar da dama na zargin cewa sakin Aminu na da nasaba da yadda rashawa ta yi wa fannin shari’ar Nijeriya kanta shi ya sa kotun ta iya ba da belin mutumin da ake zargi da aikata kisa.

Bayanai sun nuna kwanaki uku kawai Aminu ya shafe a gidan yari sannan kotu ta ba da belin sa a ɓoye bayan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu tare da raunata mutum biyu.

‘Yan’uwan waɗanda lamarin ya shafa sun yi ƙorafin cewa hatta kuɗin asibitin mutum biyun da ya kassara ko diyyar waɗanda suka mutu a haɗarin Aminu bai biya ba.

Kazalika, ‘yan’uwan sun ce babu abin da suka samu baya ga tallafin N100,000 daga Adamu Atiku Abubakar, ɗan gidan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda aboki ne ga Aminu.

A ranar Alhamis da ta gabata Kotun Majastare da ke Yola ta Kudu ƙarƙashin Alƙali Jummai Ibrahim, ta ba da umarnin a kai Aminu a ajiye a kurkuku bisa zargin kashe mutum huɗu a wani haɗari da ya auku a Yola ya zuwa ranar da za a yi zaman shari’a. Haɗarin da bayanan ‘yan sanda suka nuna ya auku ne saboda gudun wuce misali da Aminu ya yi da mota.