Kisan mijina ne ya sa na cire tsoron komai – Naja’atu Bala Muhammad

“Mace ba ta da ƙima a idon mafi yawan ‘yan Arewa”

Daga AYSHA ASAS

Masu iya magana dai na cewa, idan ka ji wane ba banza ba, ko ba a sha dare ba an sha rana. A yau shafin Gimbiya ya ɗauko ma ku ɗaya daga cikin jajurtattun mata da suka yi fice ɓangaren gwagwarmaya da kuma ita kanta siyasar. Aysha Asas ce tare da Naja’atu Bala Muhammad. Masu karatu idan kun shirya:

MANHAJA: Hajiya masu karatu za su so ki gabatar musu da kan ki.
HAJIYA NAJA’ATU: Sunana Naja’atu Bala Muhammad, an haife ni a shekarar 1956 a cikin birnin Kano a Marada, Durumin Iya. Na yi karatu har zuwa jami’a ta Ahmadu Bello da ke Zaria, Ni ‘yar siyasa ce kuma ‘yar gwagwarmaya a Nijeriya. Ni ce ‘yar siyasar Jihar Kano ta farko da ta fara zama Sanata, wacce ke wakiltar gundumar Kano ta Tsakiya. Har wa yau na kuma taɓa kasancewa ɗaya daga cikin mata na farko a Nijeriya da suka tava zama shugabar ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa daga fitacciyar Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya (ABU), sannan kuma Ni ce mace ta farko daga Arewacin ƙasar nan da ta zama Mataimakiyar Shugabar Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya ta Ƙasa (NANS).

Na fara gwagwarmaya a shekarar 1991 bayan kashe maigidana Dakta Bala Muhammad, kuma na dawo na taras da an daddatsa shi, aka yi ta zanga-zanga tsakanin ‘yan santsi da taɓo. Amma shi gaskiya ina kyautata zato dalilin da ya sa suka kashe shi ba zai wuce saboda bincike da ya yi akan zaluncin da ake yi wa talakawa na ƙwace mu su filayen su da aka ba shi aikin binciken filaye musamman na mutanen ƙauye, kamar gonakin su da dai sauransu. To ya kamata a ce an mayar musu da abubuwan su. To akan haka dai aka kashe shi, amma dai suna ta ƙaryar cewar an kashe shi saboda an ba Sarkin Kano Ado Bayero a wancan lokacin an dakatar da shi saboda ya yi tafiya ba tare da an ba shi izini ba; shi Bala Muhammad ba ruwan shi da maganar dakatarwa saboda ba shi ya bayar ba, ba shi ba ne kuma kwamishinan ƙananan hukumomi ba, saboda haka babu abinda ya haɗa shi da dakatarwa.

Saboda haka an yi amfani da wannan ne aka yi ƙone-ƙone da kashe-kashe. Ganin irin abinda aka yi masa na cin mutunci, aka kashe shi aka daddatsa shi, hannun sa ma sai bayan wasu ‘yan kwanaki aka gani. Sai na ce kawai bari in cigaba daga inda ya tsaya, na ga cewa babu wani abu da zai kuma ba ni tsoro. 

To amma kuma alhamdu lillahi, shi kansa mahaifin mu Alhaji Abdallah ɗan gwagwarmaya ne, na tashi tun ina yarinya ina ganin Baba kullum a kai shi kurkuku, ya sha wahala sosai saboda ra’ayi irin na su na cewar ba su yarda a zalunci al’umma ba; sun yi rigima da Turawan mulkin mallaka, sun yi rigima da gwamnatin da suka yarda tana cin zarafin talakawa. Idan ba don wannan gwargwarmayar da ‘yan NEPU suka yi mana ba, da mu ‘ya’yan talakawa ba mu da ikon magana, da yanzu kana nan da kai da bawa duk babu bambanci. Saboda haka an haife ni a cikin NEPU, kullum baba zai ɗauke ni ya kaini ofishin Aminu Kano, yau ina tare da Babanmu Tanko Yakasai ko gidan Shehu Sakatima ko Babba Ɗan Agundi da sauran su, haka na girma a tsakanin su.

Sannan kuma Dakta Bala Usman shi ne malamina kuma maigidana, shi ne dai komai na wa, tun daga harkokin siyasa da sauransu. Saboda haka har yau har gobe, idan ina da wata matsala a harkokin siyasa na dangana da Zariya don inje a warware min wasu abubuwan. To a gaskiya rayuwata tun daga haihuwata a cikin gwagwarmaya na rayu. Mutuwar Bala da kisan gilla da aka yi masa ya sa zuciyata ta bushe.

A rayuwata ta duniyar nan a yanzu, babu wani mahaluƙi da zan ce ina shakkarsa ko ina gudun in faɗa masa wani abu da ba haƙiƙance cewa gaskiya ce, ba na shakkar wani ɗan Adam a doron duniya. Kullum Ina addu’ar Allah Ya kashe ni kafin in haɗu da mutumin da zan ji tsoron sa.
Ni a kullum burina in haɗu da Ubangijina cikin sallama, Shi ne kawai na ke tsoro amma ba wani mahaluki ba.

Ko kin fuskanci ƙalubale a wannan tafiya ta ki?
Akan wannan gwagwarmaya Ni ma na shiga abubuwa da yawan gaske; a shekarar 2013 zuwa 2015 na zauna a Jamus saboda guba da aka saka min, hanjina ya dinga ruvewa sai da aka yayyanke aka daddasa, sai da aka yi min aiki sau bakwai saboda wannan guba da aka zuba min lokacin da muke gwagwarmaya ganin gwamnati ta kawar da Boko Haram.

Bari mu koma ɓangaren iyali. Ki na da yara nawa?
Alhamdu lillahi! Ina da yara biyar da jikoki kamar guda takwas.

Mu ji wasu daga cikin irin nasarorin da kika samu a rayuwarki.
Duk wani abu da bawa zai so a rayuwarsa, Allah ya yi min. Shekara 66 na ke da a duniya, alhamdu lillah, Allah ya yi min komai. Da farko dai mahaifina ɗan kasuwa ne, a kasuwanci aka haifeni. Ba mu san komai a gidanmu sai kasuwanci. Asalima ina ‘yar sha ɗaya da haihuwa na fara kasuwanci. To na samu cigaba matuƙa. Yanzu haka ina ciyar aƙalla mutane 200 ne. Wannan ne babban nasara ta. Kuma na tallafa wa mutane da dama ta sanadiyyar gidauniyar da na ke da ta Naja’atu Muhammad masu matuƙar yawa. Ni dama ban san amfanin kuɗi ba in har ban taimaki marasa ƙarfi ba. Alhamdu lillah.

Shin a cikin ‘ya’yanki ko akwai wanda ya bi sawunki ta fuskar gwagwarmaya?
Ba ɗaya daga cikin ‘ya’yana da suka biyo ni ta wannan fuskar. Dalilin faruwa haka kuwa ababe ne biyu; Ni ubana kamar yadda na ce shine ya yi ƙoƙarin mayar da Ni wannan matsayi da na ke a yanzu, amma Ni ban yi wa ‘ya’yana ba. Ban yi masu irin wannan renon ba, saboda Ni ce uwa, Ni ce uba, Ni ce malama, Ni ce direba, Ni ce kuku, don haka ƙarfin na wa dukka sai na yi ƙoƙarin ganin na matsa masu kan tarbiyyarsu da karatunsu, kai har ma da mu’amalarsu ta rayuwa. Ina ta gudun ‘ya’yana su yi aikin gwamnati. Tarbiyya ce don su kauce wa waɗannan ababe, su tsayu da ƙafafunsu. Duk da cewa Ni ma irin wannan tarbiyyar mahaifina ya yi min, na rashin dogaro da kowa.

Kuma cikin manyan dalilin su kan su suna tsoron wannan layin da na ke kai. Ni kaina suna fargaban abin da zai iya samuna. Akwai ma lokacin da suka haɗa kansu, suka zo suka same Ni, “Umma don Allah ki daina harkar siyasan nan. Saboda mu na son ki da rai. Ba ma so a kashe ki.” Kullum suna faɗar tsoron abin. Da kuma ababen da suka faru ta sanadiyyar gwagwarmayar, suka yi tasiri gare su. Shi ya sa gaskiya duk cikin yarana ba mai sha’awar abin da na ke yi.

Al’ada ta malam Bahaushe, zai yi wahala ka samu ‘ya ko ɗa ɗaya kawai a gida. Sai ga shi a na ku gidan ba a jin sunan kowa sai na ki. Shin ku nawa ne a wurin mahaifin na ku?
Mu goma sha ɗaya ne, amma duk yawanci sun rasu. To kuma abin da ya sa na fi kusanci da babanmu, shi wanda aka fara haihuwa kafin Ni, Allah ya jarrabe shi da cutar Foliyo, shi yaya Abdulwahabu Allah ya jiƙansa, tun yana kusan shekaru uku, sai baba ya ji ba ya son ya tashi da aƙidar shi ba kowa ne ba, wato rayuwar ƙasƙanci kamar yadda ake wa masu nakasa, to shi ne fa ya kai shi Ƙasar Burtaniya. Kuma indai ba ya zo hutu ya tafi ba, ya kai shekaru talatin a can. Wannan ya sa na zama Ni ce babba.

Kuma ba ki samu wariyar jinsi ba daga gare shi, kasancewar ki mace kamar yadda ake yi a wasu gidajen Arewa ba?
Ina, ko kaɗan. Mu ai a gidanmu babanmu ba ya bambanta mace da namiji. Aikin duk da zai sa ɗa namiji, shi zai sa mace. Kinga idan mu ka tashi a gidan babanmu, mu ne shara, babanmu na da dawakai masu yawa, kuma gidanmu mai girma ne sosai. Mu ne gyaran doki, mu ne wanke mota. Duk da cewa mu na da ma’aikata gidanmu guda biyar a kowanne lokaci, to amma da mun zo hutu, baba sai ya ba su hutu su ma, sai kuma aikin ya dawo kan mu. Wato baba ya ƙarfafa mu. Za ka yi shara, za ka yi daka, za ka yi markaɗe, za mu gyara dawakai, har mankin mota, abin da na fi tsana ma kenan (dariya) a ce yau Ni ce mai ranar wanke motaci, ko kaɗan ban son wannan aikin. Amma dole sai ka yi.

Baba ya mana wata irin tarbiyya da ba a ko ina ne za ka same ta ba. A kullum yana ƙarfafa zuciyarmu kan neman na kai tare da nuna mana ba kowa mu ke ba yanzu don a ƙarƙashin inuwarsa ce mu ke tinƙaho ba ta mu ba. Baba ya yi ƙoƙari, Allah ya yi masa rahma.

A matsayin ki ta mace kuma ‘yar arewacin Nijeriya, wane irin ƙalubale kika fuskanta a lokacin da kika zaɓi wannan hanyar ta zame ma ki ta ki rayuwa?
Ai ba abin da ba a ce min ba, domin akwai ma waɗanda ke ganin Ni kafira ce, Ni fasiƙa subhanallah!, Tun suna cewa haramun ne abin da na ke yi har aka kai ga Malaman su karen kan su, za su zo min da neman shawara, ya na ke tunanin za a ɓullo wa wannan lamari, Naja ta ina kike ganin ya kamata a taimaka mi ki a tafiyarki, na kan ce yaushe na zama Mujaddada kuma da sauransu. Abin da na fahimta da ɗan Arewa, shi asalin ɗan Arewa mafi yawansu mace ba ta da ƙima a idonsu, ta zama tamkar takalmi a wurinsu, kamar yadda Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo Allah ya qara masa yarda ya faɗa a cikin dalilan da ya sa suka yi jahadi, ya ce, “an maida mata tamkar tukwane” a yi amfani da tukunya ne, a ɗora girki a ci, a biya buƙatar abinci kawai, sai kuma an sake buƙatarsa. Don haka abubuwan ba su taɓa damuna ba, saboda ba na buƙatar yardar kowa sai ta Allah S.W.A. Ina iyakan ƙoƙari na ganin na tsaya a ikar da Ubangijina ya aje ni. Domin idan har ka ce abin da ɗan Adam ke so za ka yi, to ba za ka taɓa yin komai a rayuwarka, kuma ba za ka taɓa yi ma sa daidai ba.

Na sani a wannan tafiya ta mu ta siyasa, an wayi gari wasu da yawa cikin mata ‘yan’uwana da suke cikin harkar siyasa, suna amfani da jikinsu don samun biyan buƙata, Subhanallah! Su zubar da mutuncinsu don su samu biyan buƙatarsu.

Wane abu ne ba za ki manta da shi ba, kuma kike tuna wa da shi ki yi alfahari?
Tabbas akwai. Na taso a tsakanin arziki da matsanancin talauci, abin da na ke nufi, mahaifina ya kasance cikin masu arziki da aka san da su. Mahaifiyata tun ina shekara huɗu suka rabu da mahaifina, hakan ya sa na zama uwa ga ‘yan ƙanena, zan iya cewa ni ban taɓa wasan ƙasa ba, saboda tun ina ƙarama na ke kula da ƙanena. To ita mahaifiyarmu tana ɓangaren masu matsanancin rashi.

Ban taɓa sanin rashi a gidan mahaifina ba. Ba zan manta ba, a wata rana na je wurinta, sai na tada ita a jakin bane, to mahaifiyarmu ta kasance fara, kyakkyawar mace sosai, sai na ga ta yi baƙi, idonta ya yi jawur, sai na tambaye ta, mama me ya same ki. Ta ce, Bebi tun jiya ban ci abinci ba,(tana ce mun Bebi don ni ‘yar fari ce). Na ce, ba ki ci abinci ba, mai ya sa, shine fa take sanar da ni, dama kwano biyu ne ake kawo mata daga gidan ‘ya’yan ‘yan’uwanta biyu. To ba ta ci abinci ba saboda ba a kawo kwano ɗaya ba, don sun yi faɗa da ƙanwata wadda take matsayin abokiyar wasansa, sai ya ce a daina kawo abincin, saboda haka abincin nan na gida ɗaya, shi ta raba, qanena su ci rabin da daren, sauran rabin ta ɗumama masu suka ci da safe. Sai da ta yi kwana biyu a haka. Don ta ba wa ‘ya’yanta abincin ta haƙura tsayin kwanaki biyu.

Na ce ba ki ci abinci ba mama! kar ki damu, zan gina ma ki gida, zan ɗauke ki daga nan, zan kuma kaiki Makka. Sai ta yi dariya, can kuma sai ta fashe da kuka. Ta ce Bebi yaushe? Na ce kwanan nan. In taƙaice ma ki zance, ina koma wa makaranta, dama gwamnati na ba wa ɗalibai sabulu yankan qusa duk Juma’a. To akwai yaran masu shi, kuma lokacin Omo ya zo, da yawa ba sa son amfani da shi. Ni kuma sai na dinga bi ɗaki ɗaki ina nemo waɗanda ba sa son sabulun su ba ni. Sai da na yi bokiti biyu da sabulun.

To sai na je ƙofar makaranta, na roƙi baba mai gadi ya kaimun shi ga mamanmu. Na yi masa bayani, na ce, ya ce mata na ce, ta ɗora wa ƙanena, su fara siyarwa. To a nan na fara. Kuma shekara uku zuwa huɗu da furucin da na yi, na kai ta Makka. Na kuma gina mata gidan da ta ke ciki jim kaɗan bayan haka.

Bari mu je ɓangaren kwalliya.
To, ni fa ‘yar gayu ce kin gan ni nan. Kin dai gani (dariya) ba abin da ya dame ni. Nan da ki ke gani na, abincin da na ke ci ma ya fi na duk gidajen gwamnati da na taɓa shiga.
 
To madalla.Mun gode sosai.
Ni ma na gode.