Kisan mummuƙe ake yi wa Arewa

Daga NAFI’U SALISU

Sannu a hankali munanan abubuwa suna ƙara wanzuwa a Arewacin Nijeriya, irin abubuwan da suke da alaƙa da ɗaiɗaita ci gaban ƙasa, ko yankin ƙasa tare da alummar da suke rayuwa a cikin wannan wurin.

An daɗe ana shirye-shiryen yadda za a rusa Arewacin Nijeriya, ta yadda za a maida ita tamkar Kufai (garin da ya tashi ya zam kango babu kowa a cikinsa). A cikin manyan Malamanmu na addinin Islama, Dakta Bin Usman ya taɓa yin wata lakca da a cikinta ya yi bayani na aƙalla awa da mintina 15, inda ya bayyana wasu abubuwa na qulla-ƙulla da ake yi wa Nijeriya (musamman yankin Arewa). A qalla yau shekaru 13 zuwa 14 da na saurari wannan lakcar ta Bin Usman, wanda a ciki yake bayanin yadda suka sami kwafin wasu takardu a jihar Legas, a yayin da suke gudanar da wani bincike, takardun da suka samu suna ɗauke ne da wata Agenda ta rusa Arewacin Nijeriya, kuma an shirya ƙullalliyar ne tun kafin Nijeriya ta samu yanci, wanda a yau ana maganar shekaru 63 da samun yancin kan Nijeriya daga Turawan mulkin-mallaka na ƙasar Burtaniya.

Haka-zalika akwai mutane da dama waɗanda a lokacin da suke matasa, sun sha nuna baƙin cikinsu, da hassadarsu a kan ci gaban Arewacin Nijeriya. Akwai wanda ya riqa tada jijiyar wuya a kan bai yarda Nijeriya ta zamo ƙasa ɗaya alumma ɗaya ba a wancan lokacin, amma kuma sai da yazo ya zama shugaban ƙasar Nijeriya, kuma ƙuri’un da ya samu a Arewacin Nijeriya bai samu kwatankwacinsu a yankinsa na kudu da ya fito ba. Wannan yana nuna cewa duk da waccan magana da yayi, da yiwa Arewacin ƙasar nan zagon ƙasa, tare da nuna ƙyashi da hassada kan zamowar Arewacin Nijeriya babban yankin da Nijeriya ke tutiya da tinƙaho da shi.

Muna da shugabanni na mulkin soja da na farar hula da suke da kishin ƙasa, waɗanda suka kasance yan Arewacin Nijeriya da aka yi wa kisan gilla, waɗanda an shaida cewa suna da kishin ƙasar nan, haka kuma sun bayar da jininsu da lokacinsu tare da sadaukar da rayuwarsu don Nijeriya gaba ɗaya taci gaba, ba wai iya yankin Arewacin ba, to amma maƙiya Arewa suka sha alwashin ganin hakan bai yiwu ba.

Misali, idan muka dubi shugabancin Ahmadu Bello Sardauna, da Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa, waɗannan bayin Allahn sun yi gwagwarmaya tare da sadaukar da rayuwarsu don ganin Nijeriya ta ci gaba, irin cigaban da za a riqa bugawa a jaridu. Duk da kasancewarsu yan Arewa, amma hakan bai sa su nuna ƙabilanci, kyara ko hantara ga waɗanda ba yan Arewa ba.

Sannan idan muka dubi General Murtala Yakubu Ramat, wanda shima aka yi masa kisan gilla saboda zalunci da hassada gami da baƙin cikin kasancewarsa mutumin Arewa, kuma shugaban ƙasar mulkin soja wanda yake da kishin Nijeriya. Haka nan mu kalli yadda General Sani Abacha ya tafiyar da mulki a Nijeriya cikin tsari, babu tsoro da faɗuwar gaban cewa wata ƙasa ta Yahudawa za ta yi masa karan-tsaye dangane da shaanin ƙasarsa Nijeriya, amma shima haka aka shirya masa tuggu aka yi masa kisan mummuƙe.

Bayan rasuwar General Sani Abacha a shekarar 1999, an shirya kashe Manjo Janar Hamza Al-Mustapha, amma Allah bai yarda da hakan ba har zuwa yanzu. To amma tsarewar da aka yi masa tana da alaƙa da kassara Arewacin ƙasar nan, domin kowa yasan shi ne babban Dogarin Marigayi General Sani Abacha, kuma yasan duk wani sirri na shi Marigayi Abacha da ya shafi ci gaban ƙasa da tsarin mulki na soja mai cike da bin doka da oda. Daga wannan lokaci aka fara fito da abubuwa da dama da suke nuni a zahiri an shirya kashe Arewa.

Misali; ƙirƙirar ƙungiyar taaddanci ta Boko Haram wadda aka fito da ita daga gabacin Nijeriya wato jihar Borno. Jihar Borno jiha ce mai tarin Malaman addini da ɗaliban ilimi, domin kuwa bincike ya nuna cewa mahaddatan Alƙur’ani maigirma da ke Maiduguri kaɗai, sun fi na ƙasar Saudiyya yawa. Sannan Borno ita ce ƙasar gabacin Nijeriya mai iyaka da ƙasashe biyu, Nijar da Chadi da suke yankin sahara.

Sannan sai jihar Zamfara da ke da dazuka da tsaunika masu ɓoye da maadaina a ƙarƙashin ƙasa. An yi amfani da wasu ƙabilu wajen cika wancan mugun nufi na shirin ƙassara Arewacin Nijeriya, wanda a yanzu gashi nan zahiri mutane suna gani. Domin hatta yara ƙanana sun san menene garkuwa da mutane, sun ɗanɗani uƙubar gudun hijira daga garuruwansu da waɗancan ƙabilu suka riƙa tasa da ƙarfin tsiya ta hanyar yin amfani da makamai na zamani.

Kashe manyan Malaman addinin Islama yana daga cikin kisan mummuƙen da aka shiryawa Arewacin Nijeriya. Haka-zalika akwai sauran abubwaun da duk ana yin su ne don ƙassara Arewa, irin su; kashe ilimi, rashin kula da makarantu, asibitoci, hanyoyi da sauransu. Ba ma batun mutanen karkara a ke yi ba, waɗanda sun rasa duk wata kulawa ta Gwamnati, domin ko ɗan Jarida ne yaje ƙauye yin rahoton yadda suke gudanar da rayuwarsu, to za ka ji idan aka zo batun cin moriyar Gwamnati za su faɗa maka cewa babu wata moriya da suke ci a wajen Gwamnati, idan ma har akwai to sai dai ace idan lokacin siyasa yazo, su yan siyasar kan kazo musu ziyara sau ɗaya ko biyu tare da neman goyon bayansu a kan cimma muradunsu, dazarar kuma Ungulu ta biya buƙatarta, to sai Zabuwa ta tashi da zanenta.

A Arewacin Nijeriya ne ake yin noma da kiwo mai tarin yawa, kuma ko ƙasar ma gaba ɗaya an ginata ne da arzikin noma da kiwo da aka yi a ƙarnin da ƙasar ke cike da gaskiya da amana da ƙaunar juna. Amma a yau noman baya yiwuwa, kasuwancin ma sai da kyar. Babu ilimi, ba tsaro, ba kiwon lafiya, ba ingantattun hanyoyi, ga ƙarancin ruwan sha, ba wutar lantarki.

Yau litar man fetur da ake haƙo shi a ƙasarmu Nijeriya ma ya zamo masifa ga alummar Nijeriya. Sakamakon haka gas shima yayi kuɗi, ba batun kalanzir ake yi ba wanda yanzu ma wani ya manta yaushe rabon da yayi tozali da shi da idonsa. Rayuwa tayi matuƙar tsada, ta yadda hakan yake haifar da rasa rayukan alumma, mace-macen aure, kisan gilla, sace-sace, karuwanci, cin hanci da rashawa, halasta kuɗin haram da sauransu.

Babban abin ɗaure kai da tashin hankali da ya kamata ayi lura dashi shi ne, duk halin da ake ciki a yanzu a yankin Arewacin Nijeriya, amma wakilan alumma da suke ikirarin suna yin aiki ne don alummar qasa, amma sun tare a birnin tarayya Abuja (musamman yan Arewa) suna shaƙatawarsu, ba sa yin ta alumma ta kansu kawai suke da iyalansu.

Amma batun alummar da suke wakilta kuwa sam! Sun saka labulen baƙin ƙarfe ta yadda ko motsin giftawarsu ba za su iya gani ba, balle su sa ran cewa za su zo gare su su sauke nauyinsu da ya rataya a wuyansu.

Kowa ya gani a kwanannan abinda ya wakana na batun sayen motocin alfarma ga su yan zaman ɗumama kujerar, wanda aka riqa sokar alamarin. To da wannan zaka fahimci cewa, shin suna aiki ne don alumma ko kuwa suna yi ne don muradun kawunansu? Domin inda yan majalisa suna aiki ne don alumma, to duk abinda alummar da suke wakilta suka nuna basa buƙatarshi, to za su watsar da su. Amma su suna batun rabon motocin alfarma, ana kashe mutanen birni da karkara.

Mutumin birni a yi masa fashi da makami a gida ko a hanyar zuwa gida, shi kuma mutumin ƙauye a dira garinsa a kashe, a sace, a buge, a ƙona masa amfanin gona. Idan matafiya suna cikin tafiya a hanya a tare su, a buɗe musu wuta, ko a kwashe su a tafi daji dasu kamar wasu dabbobi sannan a nemi kuɗin fansarsu a wajen iyalansu. Duk waɗannan abubuwan fa a zahiri suke faruwa a ƙasar nan ba wai a cikin shirin fim ba, amma su yan majalisun me suke yi? Ina kuma iyalansu? Shin matansu ne kawai mataye abin so da alfahari? Shin yayansu ne kawai yayan so da qauna banda sauran yayan alumma?

Don haka ya kamata duk wani ɗan Arewa ya dawo cikin hayyacinsa. Ya zama dole kowa ya tashi tsaye yaje yayi karatu, kuma yayi hakan da saka kishin ƙasa. Domin idan ma kana neman ilimin babu kishin ƙasa a ranka to aikin banza ne. Dole mu zamto masu kishin ƙasa, mu kasance masu bin doka da oda, kiyaye dukkan wani abu da zai taɓa mutuncin yankinmu na Arewa da ƙasarmu, da kawunanmu baki ɗaya, wanda hakan shi zai sa koda a lokacin zaɓe mu zaɓi mutanen kirki waɗanda muka tabbatar da cewa suna da kyakkyawar manufa ta ci gaba da samun salama ga yan ƙasa.

Amma a irin wannan rayuwar da muke yi ta rashin sanin ciwon kai, da rashin mutunta juna, da rashin kiyaye dokar ƙasa, to lallai ba zai kai mu ga tudun mun tsira ba. Abin lura da hankalta ne a gare mu, mu kalli yadda mutanen kudu idan sun zo Arewa suke tsayawa suyi aiki tuƙuru, ko yin sanaa komai ƙanƙantarta, wadda da ita za su riƙe rayuwarsu, basa bara, basa tumasanci, sannan yayansu suna zuwa makarantu masu tsada, sannan su biya musu kuɗin makaranta tare da sauran abubuwa da ƙaramar sana’ar da yawancinmu muke rainawa. To ƙin yin sanaar da matasa suke yi saboda raina sanaar, shima wani babban balai ne ga durƙushewar garinka, jiharka, yankinki da rayuwarka kai kanka.

Nafiu Salisu Marubuci ne kuma manazarci. Ya rubuto ne daga jihar Zamfara. [email protected]
[email protected]
Tel:08038981211-09056507471