Kisan Ummita:  Ɗan Chana ya kammala kare kansa a gaban kotun Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan ƙasar Sin ɗin nan mai shekaru 47, Mista Frank Geng-Ƙuangrong, wanda ake zargi da kashe budurwarsa ‘yar Nijeriya, Ummukulsum Sani, wadda aka fi sani da Ummita, mai shekaru 22, ya kamala gabatar da shaidun kare kansa a gaban wata Babbar Kotun dake Jihar Kano.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa wanda ake ƙarar da ke zaune a Railway Quarters Kano ana tuhumarsa da aikata laifuka guda ɗaya na kisan kai.

A zaman da aka yi ranar Alhamis, Lauyan da ke kare wanda ake ƙara, Muhammad Dan’azumi ya shaida wa kotun cewa mai bayar da shaida na biyu, Dokta Abdullahi Abubakar, likitan Urologist, shi ne shaida na ƙarshe a shari’ar.

“Ina so in nemi ranar da za a iya amincewa da rubutaccen adireshin ƙarshe,” inji shi.

Tun da farko, Frank a yayin da mai gabatar da ƙara ya yi masa tambayoyi, Darakta mai shigar da ƙara na Jihar Kano (DPP), Misis Aisha Mahmoud, ta shaida wa kotun cewa ba da niyya ya dava wa Ummukulsum wuƙa a wannan rana ba.

“Ummukulsum ta kai mani hari da wuƙa, a lokacin da nake kare kaina sai ta cije ni a hannu da yatsana, sannan ta kuma raunata ni a ƙasan marata,” inji Frank.

A cikin shaidar, lauyan masu ƙara Dan’azumi ya jagoranta, Dr Abubakar ya ce: “Idan aka daɗe ana matsa lamba akan jijiyoyi na ƙarshen, ji na iya canzawa kuma sakin adrenaline ya faɗi saboda ƙarfin jijiyar Vagus wanda ka iya haifar da matsala.

“A cikin jikin mutum, ido, hanci da kunne sune jijiyoyi masu aiki na ƙarshe dake da muhimmanci ga jikin mutum.

Mai gabatar da ƙara ya yi zargin cewa wanda ake ƙara a ranar 16 ga Satumba, 2022, ya daɓa wa marigayiyar wuƙa a gidanta da ke Janbulo Quarters a Kano.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.

Laifin, inji shi, ya saɓa wa tanadin sashe na 221(b) na kundin laifuffuka.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, masu gabatar da ƙara sun rufe ƙarar da ake tuhumarsa da shaidu shida a ranar 21 ga Disamba, 2022.

Mai shari’a Sanusi Ado-Ma’aji, ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 31 ga watan Mayu domin amincewa da rubutaccen jawabi na ƙarshe.