Ko ƙuri’ar kwamitin sulhu za ta taimaki Gaza?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Wannan mako na so yin rubutu ne kan ɗan karen tsada da kujerar aikin hajji ta yi a nan Nijeriya da kai tsaye ta doshi Naira miliyan 8.5 amma nasarar ƙuri’ar neman dakatar da buɗe wuta nan take a Gaza da ta gudana a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya sa sawun giwa ya take na rakumi. A gaskiya wannan babban labari ne da ya dau hankalin duniya kuma hatta mummunan hari kan gidan rawa a Rasha bai sha gaban wannan labarin ba. Duk kokarin tsagaita wutar musamman don Gazawa su huta a cikin watan nan na Ramadan ya ci tura. Al’ummar zirin na rayuwa cikin mafi munin ƙunci. Baya ga barazanar rasa ran su a koyaushe ga kuma ƙarancin abinci da rashin muhalli.

Duk ƙoƙarin da ƙasashen duniya masu tausayawa Falasdinwa su ka yi don samun maslaha ya faskara. In kun tuna har kotun duniya Afurka ta kudu ta kai ƙarar Isra’ila don neman tsayar da kisan ƙare dangi amma hakan bai yi tasiri ba duk da hukuncin kotun na neman lallai Isra’ila ta guji hallaka waɗanda ba su ji ba ba su kuma gani ba.

Jakadan Falasdinu a Majalisar Ɗinkin Duniya Riyad Mansour ya zubar da hawaye bayan nasarar kaɗa ƙuri’ar amincewa da dakatar da buɗe wuta a kwamitin tsaro na majalisar.

Amurka ta kauracewa kaɗa ƙuri’ar don ba da dama ƙudurin ya samu nasara inda sauran membobin kwamitin 14 su ka amince.

Riyad Mansour ya ce an dau tsawon wata 6 a na gwagwarmaya inda fiye da Falasɗinawa 100,000 su ka rasa ran su yayin da miliyan 2 su ka rabu da matsugunan su.

Ƙasashen duniya masu tausayawa Falasɗinawa na nuna farin cikin nasarar kaɗa ƙuri’ar.

Amurka dai a baya ta riƙa hawa kujerar na ki da ya hana ƙudurin nasara amma yanzu dai alamu na nuna ta ɗau sabuwar matsaya.

Duniya ta tabbatar da yadda Amurka ke ɗanyen ganye tun a tarihi da Isra’ila amma yanayin kafewa kan matsaya mai tsanani da Netanyahu ke yi ya sa Shugaba Biden tsargar ɗabi’un sa da kuma ya zama wajibi ya riƙa cizawa da hurawa a mara bayan da Amurka ke yi wa Isra’ila. Duk wanda ya lura da siyasar Amurka zai ga ta na sara da duba bakin gatari in ka ɗebe kan lamarin dangantaka da Isra’ila. Haƙiƙa in ba Isra’ila ba ba wata ƙasa a duniya da za ta gwale Amurka kuma diflomasiyya ta ɗore. Wani lokacin sai ka ga tamkar abun da Isra’ila kaɗai ta ke so ne manyan ƙasashen yammancin duniya ke bi sau da kafa.

Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce ya ƙarfafa dangantaka da Amurka a matsayin mai muhimmanci ga Isra’ila.

Gallant na zantawa ne da manema labaru a ziyarar jami’an Isra’ila birnin Washington.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da dangantaka tsakanin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Joe Biden ta yi tsami.

Shugaba Biden ya fara gajiyawa da tsaurin ra’ayin Netanyahu musamman kan dagewa sai ya kai hari kan Rafah.

Kazalika ƙaurace wa kaɗa ƙuri’a ko hawa kujerar na ƙi da Amurka ta yi da ya ba da damar nasarar kuri’ar tsagaita yaƙin Gaza a kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya ya tunzura Netanyahu.

Haƙiƙa Isra’ila ce mafi cin riba a dangantaka da Amurka ta dukkan fannoni musamman tsaro da tattalin arziki ko siyasar duniya.

Za a yi tsammanin zaman sulhu ko yarjejeniya mai ma’ana ta tsagaita wuta tsakanin HAMAS da Isra’ila. Idan kuwa hakan ya gagara to a gaskiya tagomashin da Isra’ila ke da shi a faɗin duniya ya fi na kowace kasa. Shi dai kwamitin sulhun nan ya fi kowane kwamiti ƙarfi a majalisar ɗinkin duniya. Matuƙar ɓangare ɗaya ya bijirewa dakatar da buɗe wuta to fa za a yi sa ran matakai masu tsauri kan sa.

Misali ya dace a nan Amurka ta dakatar da tallafin makamai da mara baya marar misali ga yaƙin na Gaza. Kuma ya dace sauran ƙasashe irin Rasha da Sin su shigo yaƙin don kare waɗanda a ke zalunta. In kun ga hakan bai yiwu ba to matsayin na Isra’ila a siyasar duniya ya zama gagarau. Isra’ila kan ce yaƙin na ta na kare kai ne duk da yadda ta shafe shekaru ta na gasawa Falasɗinawa aya a hannu. To ma wane kare kai ne a mamayar yankunan da ba ƙasar Isra’ila ba.

Kun mamaye ƙasar Falasɗinawa ku na cigaba da gallaza mu su kuma ku na son sai lallai su yi shiru. Wannan ya sa HAMAS ke cewa yaqin ta da Isra’ila ba ya faro daga harin da ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 ba ne: gwagwarmayar na nan don kusan kullum sai Isra’ila ta gallazawa wani Bafalastine baya ga maƙare gidajen yarin Isra’ila da Falastinawa.

Duk da kaɗa ƙuri’ar neman dakatar da buɗe wuta nan take a Gaza a kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya bai hana Isra’ila kai miyagun hare-hare ta samaniya kan Rafah ba.

Sabon harin ya dira kan gidaje huɗu kuma a gida ɗaya ma daga ciki mutum 11 ‘yan uwan juna sun rasa ran su.

Mussa Dhaheer wanda mazaunin Rafah ne ya ce karar boma-bomai ta farkar da shi inda ya ga ‘yar sa a firgice ya je ya duba mahaifin sa mai shekaru 75 da mahaifiyar mai shekaru 62 da wasu abokai da su ka taho gudun hijira daga garin Gaza sun mutu a harin.

A wani bigiren harin wani Bafalsdine Jamil Abu Houri ya ce hakan na nuna rainin da Netanyahu ke yi wa majalisar ɗinkin duniya.

Hare-haren sun jawo fargabar tsayawa kai da fata na Netanyahu na lallai sai ya kawo harin mamaya ta kasa kan Rafah duk da gargaɗin kar ya yi hakan daga babbar aminiyar Isra’ila wato Amurka.

Netanyahu na caccakar Amurka kan matakin barin qudurin tsagaita wuta na nan take ya yi nasara.

Zuwa yanzu a zirin Gaza kadai Isra’ila ta kashe fiye da Falastinawa 32,000.
Hakika an tabbatar akwai dubbai da ƙasa ta danne sanadiyyar boma-bomai da Isra’ila ke saukewa.

Babban sakataren majalisar ɗinkin duniya Antonio Guterres ya yabawa Masar kan yunkurin ta na tallafawa Gaza.

Guterres ya gana da shugaban Masar Abdelfatah Elsisi inda ya nuna farin cikin matakan na Masar.

Guterres ya zayyana al’umma Gaza da cewa su na rayuwa a qunci da yunwa.

A ganawar a birnin Alkahira, Guterres da Elsisi sun ƙarfafa cewa kafa ƙasar Falastinawa a gefe da Isra’ila shararrar hanyar samun salama mai ɗorewa.

Antonio Guterres ya nuna damuwa ga yanayin ƙuncin da Falastinawa ke ciki a garin Rafah.

A halin yanzu dai kusan mazauna Gaza miliyan 1.5 cikin miliyan 2.3 na rakube ne a Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar.

Guterres wanda ya tsaya kan iyakar Rafah ya ce ya kamata duniya ta nunawa al’ummar yankin cewa ba a yi watsi da za su ba.

Kazalika Guterres ya buƙaci farfaɗo da asusun kulawa da ayyukan tallafawa Falastinawa ga lamuran jinkai.

A makon jiya ministocin wajen ƙasashen Larabawa sun sauka a babban birnin Masar wato Alkahira don tattaunawa kan gano bakin zaren warware yakin Gaza.

Tuni ministan wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya isa don zama da sauran takwarorin sa kan yanayin damuwar yaƙin na Gaza da ke cigaba hatta a cikin azumin nan.

Shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken na cikin baki masu muhimmanci ga taron.

Muradin zaman shi ne samun tsagaita buɗe wuta da kuma batun kafa ƙasar Falasdinu mai helkwata a gabashin birnin Kudus.

Tun shigar Blinken Saudiyya ya kawo batun kudurin tsagaita wutar kan Gaza. Ga shi kuma Amurka ta kawar da ido inda ƙudurin ya samu nasara. Yanzu lokaci ne na zura ido don garin tasirin cimma wannan nasara.

Ƙasar Masar da Katar ke kan gaba wajen batun sulhu tsakanin Isra’ila da HAMAS. A na sa ran dawowa zama wa imma a birnin Alkahira ko Doha. Mafi muhimmanci a lamarin nan shi ne dakatar da barazanar kai harin ƙasa kan Rafah don fargabar yadda hakan zai shafi dubban fararen hula da ke rayuwa cikin takaici. Abu mai biyewa hakan baya shi ne shigar da abinci da magani yankin Gaza don ceto waɗanda kusan za a ce na halin rai kokwai mutu kokwai.

Bakin ƙasashen duniya ya zo ɗaya kan sulhu zai tabbata ne da kafa ƙasar Falastinawa mai ‘yanci a gefe da Isra’ila. Wannan buƙata kuma ta yi hannun riga da muradun gwamnatin Isra’ila. Haƙiƙa Isra’ila ba ta son jin batun kafa ƙasar Falastinawa ta fi son a cigaba da zama yankin Falasdinawa na zama tamkar sansanin ‘yan gudun hijira da ke ƙarƙashin mulkin Yahudawa.

Da alamu yanda jam’iyyar Fatah ta shugaban Falastinawa Mahmoud Abbas ke tafiyar da mulkin Falasdinawa daga birnin Ramallah ya fi soyuwa ko samun sassaucin hulɗa da Isra’ila. Ba don HAMAS da ke da mayaqa ba, alamu na nuna haka yankin Falastinawa zai yi ta zama shekaru aru-aru nan gaba a hannun Isra’ila da ke faɗaɗa matsugunai a yankunan Falastinawan. Tun Bafalasɗine na yaro har ya girma ya kan iya rayuwa a cikin wannan fitinar. Ya kan iya rasa ran sa ko ya kare a gidan yarin Isra’ila.

Kammalawa;

Yanzu dai za a ga yadda manyan aasashen duniya za su tafiyar da wannan kuduri na kwamitin sulhu. Daga adalcin aiwatar da ƙudurin ko tsayin daka kan samar da tsagaita wutar zai haskawa duniya adalcin manyan duniya. Mun ga yanda ƙudurin kwamitin sulhu ya yi aiki kan wasu ƙasashe kuma mu na jiran mu ga yadda wannan da ya shafi gagarumar ƙasar Isra’ila zai kaya.