Ko Biyafara ta riga mu gidan gaskiya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Haƙiƙa gidan gaskiya shi ne kishiyar gida mai ƙyale-ƙyale na duniya da filo da katifa amma yayin da mai rai ya yi filo da ƙasa ya koma gidan gaskiya kenan.

Kamar yadda masu rai kan shuɗe sanadiyyar mutuwa sai dai a haifi wasu, hakanan lamuran rayuwa su ke shuɗewa da ya sa ma a ke yi wa duniya kirari da “mai yayi” don nuna cewa komai ka gani a na yayinsa wata rana zai zama tsohon ya yi. Misalin fitina a nan Nijeriya, kun ga ai yaƙin basasa na Ojukwu ya zama tarihi haka nan Marwa Maitatsine ya zama sai tashin zance.

Zamanin yau wata fitinar ce daban da ta zo har da masu ƙunar baƙin wake da waɗanda kan tada boma-bomai har ma ga masu banka wa mutum wuta da ransa ya ƙone ƙurmus don kawai sun tsane shi ko don addinin su ko ƙabilar su ba ɗaya ba ne!

Zaman lafiya ya koma ƙamshin turaren ɗangoma don duk inda mutane su ke zaune ba da fargabar wani zai zo ya ci zarafin su ba, da sauƙi ko da ba wadatar ababen more rayuwa. Ba abun da ya fi daɗi a doron duniya irin zaman lafiya. Duk wasu ni’imomi da a kan ci moriyar su sai da zama lafiya. Idan an samu zaman lafiya sai a samu kwanciyar hankali in an samu kwanciyar hankali sai a samu natsuwa daga nan za a iya baje kolin walwala da nishaɗi.

Alƙiblar wannan mako za ta duba makomar tada ƙayar baya na wasu ’yan ƙabilar Ibo da ke son su raba Nijeriya don kafa ƙasar su a yankin da suka fi rinjaye a Kudu. Ƙalubalen wannan bahagon muradi shi ne na cusa ƙiyayya da kashe jama’ar yankin Arewa da ke yankin na su. Lamarin ya kai ga kashe jami’an tsaro da cinnawa dukiyar gwamnati wuta. Gaskiya wannan hanya na cike da yamutsi da rashin tabbas, har ma da amsa kirarin nan da ke cewa “wane wayo gare ka amma ba ka da hankali” don wanda ya ke gidan gilashi ba zai yi wasan jifa ba, sai dai ya lallaba ya samu biyan muradin sa ta hanyar hawa teburin shawara ko lamuran majalisa.

Gwamnatin Nijeriya za ta tuhumi shugaban ƙungiyar ’yan awaren Biyafara/IPOB Nnamdi Kanu da cin amanar ƙasa da kuma tunzura jama’a su yi bore da sauran su.

Wannan ya faru ne bayan iza ƙeyar Kanu ko cafke shi daga ƙetare zuwa Nijeriya don fuskantar shari’a kan ɗaukar nauyin ƙungiyar da ta riƙe makamai ta na yaƙi da jami’an tsaron Nijeriya musamman a yankin Kudu maso gabashin Nijeriya da Kudu maso kudancin Nijeriyar.

Tuni a ka gurfanar da Kanu gaban kotun Mai Shari’a Binta Nyako wacce tun farko ta ba da belinsa, amma ya yi amfani da damar wajen arcewa zuwa Israila inda daga bisani ya shiga Burtaniya.

Masana shari’a na cewa nuna Kanu zai iya fuskantar hukunci mai tsanani matuƙar a ka same shi da cin amanar ƙasa. Nnamdi Kanu na son raba Nijeriya don kafa ƙasar Biyafara ta ƙabilar Igbo da ta samo asali daga marigayi Janar Odumegwu Ojukwu da ya haddasa yaƙin basasa a 1967 har zuwa 1970 inda tsohon shugaban mulkin soja Janar Yakubu Gowon ya ayyana cewa “ba wanda ya ci nasara a yaƙin kuma ba wanda a ka ci nasara a kan sa” da zummar hikimar hakan ta zama silar haɗin kan ’yan Nijeriya, bayan asarar dubun dubatan rayuka da dukiyoyi.

Waɗanda suka mutu a yaƙin da son zuciya ya haddasa sun haɗa da mata da ƙananan yara. Duk yaƙin da ya shafi masu rauni to ba shakka yaƙi ne da ya samo sila daga mummunan lamarin da ba za a iya kauda kai ba sai an kawar da shi. Wani lokacin kuma tsananin rashin sanin ya kamata ya kan sa a rutsa da masu rauni. A lokuta ƙalilan ne hakan kan faru bisa tsautsayi ko kuskure.

Mai Shari’a Binta Nyako ta bai wa Kanu dama ya yi Magana, inda shi kuma ya yi ƙoƙarin cewa ba arcewa belin da ta ba shi don ya fice daga ƙasar don tsira da ransa sanadiyyar yadda sojoji suka kai hari yankin da ya ke a jihar Abiya. Duk da haka Kanu bai yi magana kan yadda ya ke amfani da kafafen yanar gizo wajen zuga ’yan ƙungiyarsa da a ka haramta su yi ta kashe-kashe da zubar da jinin ’yan Arewa. Ma’ana ko me ya sa Kanu bai yi shiru ba tun da ya san yana zaman beli ne?

Idan har da Kanu na mutunta kotun kamar yadda ganin ido ya sa ya cewa Jastis Nyako “mai girma mai shar’a” to da