Ko da tsiya tsiya sai mun ci zaben 2023 – Shugaban APC na Kano

APC a jihar Kano ta shirya fito na fito da PDP

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta shirya yin fito na fito da abokiyar adawar ta ta PDP a jihar.

Shugaban jam’iyyar na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake mai da martani ga wasu kalamai da tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi. Inda tsohon gwamnan ke iqirarin, za su duk abinda za su yi, su ga ba a murxe musu zaven 2023 ba a jihar.

“Ba za mu qara ragawa wani xan adawa ba a jihar nan ko wanene, ina umartar ku da ku fito ku ja daga da su ko a ina su ke a faxin jihar nan” Inji shugaban APC xin.

Ya yi wannan kalamai ne a lokacin qaddamar da sabbin zavavvun  yan kwamitin zartarwar qananan hukumomi da aka yi a gidan gwamnatin jihar. Inda ya baiwa yan jam’iyyar umarnin su dau matakin da za su iya durqusar da karsashin yan adawa ko ta wane hali.

Ya kuma qara da cewa “A zabe mai zuwa, ba za mu bari ayi zabe sahihi ba, abinda mu ka yi a Gama, shi za mu maimaita. An wuce zamanin da za a yi zave nagari, yadda mu ka yi wancan, wannan ma haka za mu yi shi. Dan  haka ina kira a gare ku, da kar ku saurara ko tausaya duk wani xan kwankwasiyya ko waye shi”

Ya qara da cewa, ko da tsiya, ko da tsiya tsiya sai mun sake cin zave a 2023″ Dan haka ya ce wa yan jam’iyya, su fuskanci yan adawa ta kafafen watsa labarai, da kuma ta hanyar daukar makami.

Ya yi kira ga Gwamna Ganduje da kar ya yadda ya baiwa yan kwaya muqami a gwabnatin sa, sannan kuma ya tunawa gwamnan cewa “Yan kwankwasiyya fa har yanzu a gidajen gwamnati su ke zaune”

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*