Ko giya na da tasiri a gyara ko lalacewar fata?

Daga AISHA ASAS

A wani littafi na bayanin yadda ake amsa tambayoyin hukunce-hukuncen Musulunci, malamin ya ce, “mai shar’antawa (Allah kenan) ba ya umurni da a yi abu har sai abin ya kasance alkhairi tsagaron sa, ko alkhairin yafi sharrin yawa. Kuma ba ya hani ga abu har sai abin nan ya kasance sharri ne tsagaron sa ko sharin yafi alkhairin yawa.”

Wannan maganar ce ta kasance ga giya, domin tana ɗauke da cutarwa fiye da alfanu ga mai shanta. Cutarwa da amfani da giya ke yi ga jiki ya shafi fata, domin tana matuƙar tasiri ga fatar jiki wanda za mu iya cewa tana cikin layin farko-farko da za su girbi shan giyar da mai ita ke yi.

Bincike ya tabbatar giya na ɗauke da illa fiye da amfani ga fatar ɗan Adam musanmman ma ga mace.

A lokacin da kika fara shan giya, ‘yar’uwa, za ki ga fatarki na ƙyalli, wata kila har ki nemi ƙurajen fuskarki ki rasa, ina zancen a watannin farko na fara shan giyar. Wannan shine kawai mora da idonki zai gani da fatarki ta yi, wanda a zahiri kenan, amma a ɓoye share fage ne na cutar da fatar.

Barasa guba ce, kuma shi jikinki ya fahimci hakan, don haka ne ke sa lokaci kaɗan zai fara bayyana maki illar da kika sanya a cikin sa. Za ku amince da zance na ne idan kuka yi duba da irin ababen da aka so mai shan giya ya lizimta, misali nama, wanda kwarai ma’abuci giya ke buƙatar abinci mai maiƙo da kuma sinadarin furotin don ganin giyar bata yi saurin bayyana ba.

Illolin giya ga fata

Bushewar fata: duk wadda ta san tana shan giya, kuma tana fama da matsalar matsanancin bushewar fata to ka da ta wahalar da kan ta yawon neman magani, domin maganin matsalar tana tattare da barin shan barasa.

Saurin tsufa: shan giya akai-akai na lalata tanadin bitamin C da E wanda ke taimakawa furotin ɗin da ke da alhakin sanyin fata. Oval na fuska kan rasa ƙarfin sa, kuma giyar na aikin zubar da ƙarfin fatar, bayan haka ta kan hana fata saurin farfaɗowa. Hakan na nufin idan ta yi ƙasa ba za ta dawo ba matuƙar ana ci gaba da shan barasar. Wannan dalilin ne zai sa fatarki ta bayyanar da tsufa fiye da shekarunki.

Don haka, ‘yar’uwa, ki sani, giya na haifar da sauye-sauye ga fatarki marasa kyau waɗanda ke da wuyar bin hanyoyin kwaskwarima. A taƙaice dai giya na haifar da sake fasalin matakan ‘homonal’ matuƙar kin bari giyar ta zame ma ki jiki, hakan zai mayar da ke a matakin girma na homon maza. Hakan zai sa fatarki tayi tsauri wanda zai sata wahalar karɓan kayan kwalliya.