Ko na faɗi zaɓen fidda ɗan takara Ina tare da PDP – Wike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, kuma gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike ya bayyana cewa a irin ƙaunar da yake yi wa PDP ba ya ganin ko ya faɗi zaɓen fidda ɗan takara zai koma wata jam’iyyar.

Wike ya ce, ”ko na yi nasara a zaɓen fidda gwani, ko ban yi ba, PDP zan cigaba da yi babu gudu ba ja da baya.”

Idan ba a manta ba gwamnan Ribas, Nyesome Wike ya fito takarar kujerar shugaban ƙasa a zaven 2023.

Sai dai kuma akwai jan aiki a gaban sa domin, akwai ‘yan takara da dama a gaban sa wanda suma kujerar ce a gaban su.

Cikin su akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Anyim Pius Anyim da dai sauran su.

Wike ya kai ziyarar ganawa da wakilan jam’iyyar a garin Minna Jihar Neja. Wike ya ce: ”Idan kuka zaɓe ni ɗan takaran ku, ku sani baku yi asara ba, domin ƙasar nan na buƙatar mutum jarimi, gogagge sannan mara tsoro.

”Nijeriya na buƙatar mutumin da idan ya ga abu fari zai ce wannan abu fari ne, babu tsoro ko fargabar wani abu zai faru.

”Wannan mutum kuma ni ne, saboda haka ina neman ƙuri’un ku a zaɓen fidda gwani da za a yi domin mu kai ga nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *