Kocin Bayern, Thomas Tuchel zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Koci Thomas Tuchel zai bar ƙungiyar Bayern Munich a ƙarshen kakar wasa ta bana.

Ɗan shekaru 50 ɗin ya maye gurbin Julian Nagelsmann a watan Maris din 2023, inda ya ƙulla yarjejeniyar har zuwa watan Yunin 2025.

Sai dai tsohon kocin Chelsea ɗin zai raba gari da ƙungiyar saboda “sauye-sauyen da Bayern ke yi”.

Tuchel ya jagoranci Bayern lashe gasar Bundesliga a kakar wasan da ta wuce amma a yanzu Bayer Leverkusen ta basu tazarar maki takwas.

Sannan kuma an doke Bayern a wasa uku a jere.

Shugaban Bayern, Jan- Christian Dreesen ya ce “duka ɓangarorin biyu sun amince a raba gari.”

“Burinmu shi ne mu samu sabon koci a kakar wasa ta 2024-25,” inji shi.

Tuchel, wanda a baya ya jagoranci Paris St-Germain da Borussia Dortmund, ya ce “Zamu bar nan a karshen kakar wasa ta bana. Amma dani da mataimaka na za mu tattabar da nasarar ƙungiyar.”

Tuchel ya samu nasara a wasa 28 sannan ya yi rashin nasara a wasa 11 cikin 44 da ya jagoranci Bayern Munich.