Korarren kwamishinanmu na Jihar Adamawa ya yi ɓatan dabo – INEC

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ce ba ta da masaniyar inda korarren Kwamishinanta na Jihar Adamawa, Hudu Ari, ya shige tun bayan abin da ya aikata yayin zaɓen cike giɓi na zaɓen gwamnan jihar.

Ari ya yi riga malam masallaci wajen sanar da sakamakon zaɓen cike giɓin da aka gudanar tun kafin kammala tattara sakamakon zaɓen.

A cewar INEC, “Ba mu san inda yake ba, saboda tun bayan abin da ya faru Hukumar ta aike masa da wasiƙa ta kuma kira shi a waya. Bai amsa kira ba, kuma shi bai kira ba.

“Mun buƙaci ya kai kansa Hukumar ranar Lahadi, ba mu gan shi, mun ce ya zo ranar Latinin ba mu gan shi ba.

“Har zuwa yanzu bai kai kansa Hukumar ba kuma ba mu san inda yake ba.”

Kwamishinan INEC na ƙasa, Fetus Okoye, shi ne ya yi waɗannan bayanan a cikin wani shiri da tashar Channels Television ta yi da shi ranar Juma’a wanda jaridar Jaridar News Point Nigeria ta bibiya.