Korona: Hukumar kula da babban birnin tarayya ta dau sabbin matakai

Hukumomin da ke kula da babban birnin tarayya Abuja, sun kafa sabbin dokokin da za su taimaka wurin dakile yaduwar cutar Korona a fadin birnin.

Ministan babban birnin tarayyar, malam Muhammad Bello ya ce, jami’ai na musamman za su kasance a kan tituna domin tabbatar da ba a kaucewa dokokin ba. Ya kuma kara da cewa, ofishinsa yana wani hadin guiwa da hukumar shari’a domin ganin kotu na sun tashi tsaye wurin ladabtar da masu kunnen kashi.

A cewar sa, yawan alkaluman wadanda su ka kamu da cutar a birnin tarayyar ya haura yadda ake zato, dan haka ya zama wajibi a dau matakin dakile yaduwar wannan cuta. Dan haka ya zama wajibi a ringa duba yanayin zafin jikin masu shiga da fice a wuraren kasuwanci da ofisoshi. Haka kuma dole kowanne mutum ya zama na yana sanye da kariyar fuska a duk lokacin da zai shiga wani wuri.

Ministan ya kuma bada umarnin cewa, ma’aikata da ba su da lafiya, ko su ka ji alamun cutar, su sanar da shugabannin su, ko kuma jami’an kula da cutar, ko su zauna a gidajen su.

“Ko da yake, wadannan dokoki ne da su ka shafi wuraren aiki, a daidai lokacin da hutu ke matsowa, akwai bukatar mu kada dokokin da za su kula da yadda za a gabatar da bukukuwa a lokacin bikin Kirismeti da na sabuwar shekara” in ji ministan.

Mista Ikharo Attah wanda shine jami’i mai kula da cutar na Babban Birnin Tarayya ya ce “za mu halarci ofisoshi, da kasuwanni da wuraren taruwar jama’a domin wayar wa da mutane kai akan wannan cuta da matakan da aka dauka don dakile ta

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*