Korona ta yi ajalin mutum milyan biyu a faɗin duniya – Bincike

Daga WAKILIN MU

A halin da ake ciki, adadin mutanen da cutar korona ta aika lahira a faɗin duniya ya kai milyan 2,441,917 kamar yadda sakamakon binciken Jami’ar Johns Hopkins ya nuna.

Haka nan, jami’ar ta ce adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan duniya ya kai milyan 110.3.

Sai dai, sakamakon binciken jami’ar ya nuna an samu raguwar adadin mutanen da kan kamu da cutar a cikin yini a faɗin duniya. Inda ya nuna a Talatar da ta gabata aka samu mafi ƙarancin adadi na waɗanda ke kamuwa da cutar a yini.

A cewar jaridar Wall Street, yanzu haka wata tawagar masana kimiyya ta Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na nan na gudanar da bincike kan wasu dabobi guda biyu, wato dabbar nan mai suna ‘ferret badger’ a Turance da kuma zomo, domin gano inda ƙwayar cutar korona ta samo asali.

Masana sun ce waɗannan dabbobi biyu suna iya ɗaukar ƙwayar cutar korona, alhali an samu ana cinikinsu a kasuwar Wuhan, China, inda a nan aka fara samun ɓullar cutar.