Kotu da ɗaure ƙasurgumin mai satar mutane, Wadume, shekara bakwai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ɗaure ƙasurgumin mai satar mutanen nan domin karɓar kuɗin fansa da ke Jihar Taraba, a Kudu maso Gabashin Nijeriya, Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume, shekara bakwai ba tare da zavin tara ba.

A shari’ar da aka shafe tsawon shekara uku kotu ta samu Wadume da laifi a kan tuhuma ta biyu da ta goma daga cikin goma sha uku da kuma wasu mutum biyu waɗanda Babban Lauyan Gwamnatin Nijeriya ya gabatar a kansu bakwai.

Laifukan da aka ɗaure shi a kai sun shafi gudu daga inda ake tsare da shi da kuma ta’ammali da haramtattun makamai.

Sauran waɗanda aka tuhuma a shari’ar sun haɗa da Aliyu Dadje, wanda Sufeton ‘yan sanda ne, da Auwalu Bala, mai laqabin Omo Razor da Uba Bala, mai laƙabin Uba Delu da Bashir Wazlri mai laƙabin baba runs da Zubairu Abdullahi mai laƙabin Basho) da kuma Rayyanu Abdul.

Kotun ta ɗaure Aliyu Dadje (Sufeton ‘yan sanda) wanda shi ne babban jami’i a hedikwatar ‘yan-sanda a ƙaramar hukumar Ibi ta Jihar Taraba shekara uku bisa laifin ƙoƙarin lalata sheda domin ɓoye laifi.

Mai shari’ar ta kuma ɗaure Delu, da Abdullahi, da Abdul shekara bakwai a gidan yari, yayin da ta wanke da kuma sallamar Omo Razor da Baba Runs sabodarashin sheda.

A ranar 22 ga watan Yuli ne Justice Nyako ta yanke hukuncin, amma sai ranar Lahadi 14 ga watan Agusta aka bayyana shi ga ‘yan jarida.